in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kudi na Sin ya halarci taron kwamitin harkokin ci gaba na bankin duniya da asusun IMF karo na 99
2019-04-15 13:53:44 cri
An gudanar da taron kwamitin kula da harkokin ci gaba na bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya wato IMF karo na 99 a birnin Washington na kasar Amurka a kwanakin baya. Ministan kudi na kasar Sin Liu Kun ya halarci liyafar tsakar rana ta ministoci masu halartar taron tare da yin wani jawabi, kana mataimakiyar ministan kudi na Sin Zou Jiayi ta halarci taron ministoci na kwamitin, inda ta gabatar da jawabi.

Liu Kun ya bayyana cewa, ya kamata bankin duniya ya tsaya tsayin daka kan ka'idojin ra'ayin bangarori daban daban, da sa kaimi ga bangarori daban daban da su nuna goyon baya ga tsarin ciniki a tsakaninsu bisa tushen ka'idojin, da samar da gudummawa ga dukkan membobin kungiyar bisa yanayin da suke ciki.

Liu Kun ya kara da cewa, a bana Sin za ta ci gaba da sassauta iznin shiga kasuwarta, da kara tabbatar da ikon mallakar fasaha, da kara rage harajin da ake bugawa kayayyaki, yana mai cewa, ta hakan za a samar da yanayin zuba jari da yin ciniki mafi jawo hankali. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China