Rahoton kamfanin dillancin labarai na kasar Syria ya ruwaito cewa, shugaba Bashar, ya gana da al-Falih Faryadi, mai ba da shawara kan ayyukan tsaron kasar Iraki, wanda ya kai ziyara kasar Syria, a jiya. Inda shugaban kasar Syria ya ce, yanayin da ake fuskanta a yankin da kasashen 2 suke ciki, gami da daukacin duniya, na bukatar kasashen Syria da Iraki su yi kokarin kare mulkin kai da 'yancin tsara manufa bisa ra'ayin kansu, a lokacin da suke fuskantar abokan gaba, wadanda ke son ganin barakar kasashen, gami da tashin hankali a cikinsu.
Ban da haka, bangarorin 2 sun tattauna hanyar da za a bi wajen kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, tare da jaddada wajibcin raya huldar daga dukkan fannoni.
A nashi bangare, al-Falih Faryadi ya ce, yadda kasar Syria ta samu dakile ta'addanci wata nasara ce a bangaren kasar Iraki, yayin da duk wani ci gaban da aka samu a matakin sojan da aka dauka a kasar Iraki, zai taimakawa samun kwanciyar hankali a Syria. (Bello Wang)