Trump ya ce, ya yarda da kalaman Kim dake cewa akwai kyakkyawar hulda a tsakaninsu, inda ya ce zai fi dacewa a yi amfani da kalmomin "matukar kyau" don siffanta dangantakarsu.
Trump yana da yakinin cewa, a karkashin jagorancin Kim, Koriya ta Arewa na da kyakkyawar makoma wajen raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma. Ya kara da cewa, nan bada jimawa ba, Koriya ta Arewar za ta zama daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya, bayan ta cimma burin kauda makamanta na nukiliyar, sannan aka soke takunkumin da aka sanya mata.
A yayin da yake ganawa da takwaransa na Koriya Kudu Moon Jae-in a kwanakin baya a fadar White House, Trump ya ce yana tunanin gudanar da shawarwari karo na uku tsakanin shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa. Ya kuma jaddada cewa, duk da cewa Amurka ba za ta yi la'akari da kara sanya takunkumi kan Koriya ta Arewa ba, ba za ta sassauta takunkumin dake kan kasar na yanzu ba.(Murtala Zhang)