Shugaban bankin duniya na rikon kwariya, Kristalina Georgieva, da babbar darektan asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Christine Lagarde da babban darektan kungiyar cinikayya ta duniya Roberto Azevedo ne suka bayyana hakan, yayin wani taron bainar jama'a da ya gudana a babban bankin duniya a birnin Washington DC na kasar Amurk.
Jami'an sun kuma bayyana cewa, tarihi ya nuna cewa, cinikayya abu ne mai muhimmanci ga ci gaba, samar da ayyukan yi da kuma rage talauci.
Don haka, muddin ana bukatar magance wadannan kalubale, wajibi ne kungiyoyin kasa da kasa kamar IMF da bankin duniya da WTO su hada kai da gwamnatocin kasashe kan wadannan batutuwa. (Ibrahim Yaya)