in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun bada ra'ayoyi kan makomar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka
2019-04-11 14:34:02 cri

A ranar 9 ga watan Afrilu ne, aka kafa cibiyar nazarin Afirka ta kasar Sin a nan birnin Beijing. A yayin taron shawarwari kan hadin gwiwa da mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar bayan bikin kafa cibiyar, masana na kasa da kasa sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda za a zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu.

Nahiyar Afirka, wani muhimmin bangare ne a kokarin da ake na raya shawarar "ziri daya da hanya daya". Mataimakin shugaban jami'ar ilmin zamantakewar al'umma ta Bamako dake kasar Mali Macki Samake yana ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta dace da muradun Sin da Afirka, jama'ar kasashen Afirka da dama sun amfana da shawarar, kana shawarar ta kara fahimtar juna a tsakanin Sin da Afirka. Ya ce,

"Shawarar 'ziri daya da hanya daya' ta shafi fannonin tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari, da ayyukan more rayuwa da sauransu, ta kuma zama wata gada dake hade Sin da Afirka, ta haka bangarorin biyu za su kara fahimtar juna, da hada kai da kuma girmama juna."

A kokarin da ake yi na raya shawarar "ziri daya da hanya daya", an gano wasu abubuwan da suka kawo cikas ga bunkasar Afirka ciki har da rashin samun ayyukan more rayuwa da sauransu. Shugaban cibiyar nazarin fasahohin sadarwa da tattalin arziki na kwalejin ilmin zamantakewar al'ummar kasar Sin Li Ping ya bayyana cewa, inganta ayyukan more rayuwa muhimman fasahohi ne da Sin ta ke kokarin samarwa a kasashen Afirka don samun ci gaban nahiyar. Ya ce,  

"A halin yanzu za mu ga cewa, Afirka tana kan matakin neman tsayawa da kafafunta, nan gaba za ta shiga matakin samun ci gaba cikin sauri. Sin tana son hada kai tare da Afirka wajen samun ci gaba da wadata ta hanyar raya shawarar 'ziri daya da hanya daya', kana Sin tana son samar da fasahohin gina ayyukan more rayuwa ga kasashen Afirka, bisa ga kokarin da ta ke yi na bunkasa kanta daga kasa mai karancin kudin shiga zuwa kasa mai matsakaicin kudin shiga har zuwa kasar da ta kai babban matsayi a fannin samun kudin shiga."

Game da makomar hadin gwiwa da mu'amalar al'adu a tsakanin Sin da Afirka, shugaban kwalejin nazarin harsuna na kasar Tunisia Elhaj Ahmed Khaled ya yi amfani da misalin mu'amalar dake tsakanin Sin da Tunisia don bada shawarar kara yin mu'amala a tsakanin jami'o'i da kwalejoji da kuma hukumomin nazari. Ya ce,

"Mun sake bada shawarar cewa, ya kamata malamai da masana na hukumomin bada ilmi su yi amfani da shawarar yin hadin gwiwa da samun moriyar juna da shugabannin kasashen biyu suka gabatar, da kara yin mu'amalar al'adu da nazarin al'adun kasa da kasa a tsakanin hukumomin bada ilmi na kasashen biyu, hakan zai taimakawa jama'arsu wajen sanin hakikakin yanayin da kasashen biyu ke ciki ta yadda za a kara samun fahimtar juna a tsakaninsu."

Shugaban cibiyar nazarin kasar Sin ta jami'ar Dar es Salaam ta kasar Tanzania Humphrey P.B. Moshi yana farin ciki da kafa cibiyar nazarin Afirka da kasar Sin, yana fatan masanan Sin da Afirka za su kara yin hadin gwiwa wajen yin nazari don shaidawa duniya hakikanin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Ya ce,

"Akwai bukatar yiwa jama'a da kamfanoni karin bayanai game da yanayin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, kana za mu yi amfani da wadannan bayanai don mayar da martani ga munanan kalaman bahaguwar fahimta da wasu ke yayatawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu. Ya kamata mu yi amfani da nazarinmu don fada musu cewa, ana samun moriya ta hanyar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China