in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashe kan karuwar tattalin arzikin duniya na 2019
2019-04-11 13:23:24 cri

Asusun ba da lamuni na kasa da kasa (IMF) a ranar Talata ya rage hasashen da ya yi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 3.3 cikin dari a shekarar 2019 a cikin sabon rahotonsa, amma hasashen ya nuna a watan Janairun shi ne kashi 3.5 cikin dari.

IMF ya ce, tattalin arzikin duniyar yana fuskantar barazanar samun komada sakamakon wasu matsalolin na rashin tabbas dake ci gaba da wanzuwa sakamakon rigingimun ciniki na duniya.

Hasashen karuwar tattalin arzikin na kashi 3.3 bisa 100 a shekarar 2019, ya yi kasa da kashi 0.3 bisa 100 na alkaluman hasashen tattalin arzikin shekarar 2018, sai kuma an yi hasashen karuwar tattalin arzikin duniya za ta kai kashi 3.6 bisa 100 a shekarar 2020.

Alkaluman karuwar manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki na shekarar 2019 kuwa, shi ne kashi 1.8 bisa 100 da kuma kashi 1.7 bisa 100 a shekarar 2020, dukkansu kasa da kashi 2 da dan kari bisa ga abin da aka samu a cikin shekaru biyun da suka gabata, a cewar rahoton.

Game da kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki kuwa, IMF ya yi hasashen samun karuwar kashi 4.4 bisa 100 a shekarar 2019, kasa da 0.1 a shekarar 2018, kuma adadin zai iya bunkasuwa zuwa kashi 4.8 bisa 100 a shekarar 2020, inda ya yi daidai da na shekarar 2017.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China