in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta karawa Burtaniya wa'adin ficewa daga kungiyar zuwa Oktoba
2019-04-11 13:05:59 cri

Shugaban majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai (EU) Donald Tusk, ya bayyana cewa, shugabannin kasashe mambobin kungiyar EU 27 da suka rage a cikin kungiyar, sun amince a karawa Burtaniya wa'adin ficewa daga kungiyar, har zuwa ranar 31 ga watan Oktoban wannan shekara.

Shugaban wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a tsakar daren jiya, bayan kammala wani taron sirrin kungiyar, ya ce, hakan na nufin yanzu Burtaniya, na da watanni 6, da za ta lalubo hanyar warware batun ficewarta daga kungiyar.

A jiya ne dai, shugabannin Turai suka hallara a Brussels, don gudanar da taron koli na musamman, kafin wasikar da firaministar Burtaniya Theresa May ta aikawa Tusk, inda ta bukaci a karawa kasarta wa'adin ficewa daga kungiyar, bisa ayar dokar kungiyar ta 50.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China