Dangane da sanarwar hadin gwiwar taron da ta jawo hankali sosai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Laraba cewa, sanarwar hadin gwiwar da kasar Sin da kungiyar EU suka fitar, ta nuna cewa, bangarorin 2 sun iya kawar da sabaninsu, ta hanyar tattaunawa da shawarwari, lamarin da ya nuna kyakkyawar huldar abota da yin hadin gwiwa da ke tsakaninsu daga dukkan fannoni. (Tasallah Yuan)