in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin Da Na Turai Na Kokarin Cimma Matsaya Daya Da Kuma Cin Nasara Tare
2019-04-10 17:00:05 cri

Bayan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping da ya kai wasu kasashen Turai uku a watan Maris da ya gabata, a kwanakin nan, shi ma firaministan kasar Li Keqiang ya mai da hankalinsa a Turai a ziyararsa ta farko a wannan shekara, matakin da ya shaida muhimmancin da Sin da Turai suka dora wa juna a harkokinsu na diplomasiyya, muhimmancin da a cewar shugabannin kungiyar tarayyar Turai "Abu mai muhimmanci da ba a taba ganin irinsa ba".

A jiya Talata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk da na hukumar gudanarwar kungiyar Jean Claude Junker yayin taron shugabannin Sin da EU karo na 21, inda kuma suka bayar da hadaddiyar sanarwa. Taron ya kasance muhimmin tsarin shawarwari da aka gudanar kawo yanzu tsakanin Sin da kungiyar tarayyar Turai, kuma a bara bangarorin biyu sun gudanar da bikin murnar cika shekaru 20 da kafa tsarin. Don haka, wannan ya bude wani sabon mafari na taron a wannan karo. A yayin taron, gaba daya bangarorin biyu sun amince da hada kai da kuma raya moriyar bai daya a tsakaninsu, lamarin da ya kawar da rashin tabbas da ake fuskanta a duniyar yau.

A 'yan shekarun nan, an fara raya sabon salon dangantaka a tsakanin Sin da Turai har ma an samu kyawawan sakamako. A shekarar 2014, a karon farko Shugaba Xi Jinping ya ziyarci babbar hedkwatar kungiyar EU, inda ya gabatar da cewa, za a raya sabuwar dangantaka a tsakanin Sin da Turai wadda ke burin samun zaman lafiya da ci gaba da gyare-gyare da ma wayewar kai baki daya, lamarin da ya aza harsashi ga bunkasar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu a nan gaba. Haka kuma a karkashin tsarin hadin gwiwa don samun nasara tare, aikin cinikayya da zuba jari a tsakanin bangarorin biyu ya samu saurin bunkasa, har ma ya sa EU ta zama aminiyar cinikayyar kasar Sin mafi girma a duniya a shekaru 15 a jere, baya ga jimillar cinikayyarsu ta shekarar 2018 ta kai matsayin koli a tarihi da ta kai dala biliyan 682.16, yayin da kasar Sin kuma ta kasance abokiyar cinikayya ta biytu mafi girma ga EU a shekaru da dama da suka wuce. A waje daya kuma, hadin kansu yana ta kyautatuwa a fannonin zaman lafiya da tsaro, samun dauwamammen ci gaba, cudanyar al'adu, da ma kirkire-kirkiren fasaha. Don haka, ko shakka babu ziyarar firaministan kasar Sin a wannan karo, za ta kara daga matsayin dangantakar da ke tsakanin Sin da Turai zuwa wani sabon mataki bisa aniyar kara tabbacinta da amfanawa juna bisa manyan tsare-tsare.

Kasar Sin da kasashen Turai sun cimma matsaya guda a fannoni daban daban, haka kuma suna da moriya iri daya, duk wadannan sun aza harsashi mai kyau ga hadin gwiwar dake tsakaninsu. A baya wasu kafofin watsa labaran kasashen Turai sun taba bayyana cewa, har kullum manufar da kungiyar tarayyar Turai take aiwatarwa kan kasar Sin tana sauyawa, to ra'ayin da ake dauka kan hadin gwiwa da takarar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ya fi jawo hankalin sassan biyu, har ma ya fi jawo hankalin daukacin kasashen duniya baki daya. Kan batun, shugabannin kasar Sin da kasashen Turai sun sha jaddadawa cewa, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya fi takarar dake tsakaninsu muhimmanci, matsaya guda da suka cimma shi ma ya fi bambancin dake tsakaninsu yawa. Yayin taron tattaunawa tsakanin manyan jami'an sassan biyu da aka gudanar kwanan baya, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi nuni da cewa, Sin da kasashen Turai sun cimma matsaya guda a fannoni goma, misali gaba dayansu suna goyon bayan tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, tare kuma da nuna rashin amincewa da ra'ayin kashin kai, kuma suna goyon bayan MDD da ta jagoranci harkokin kasashen duniya, tare kuma da kiyaye ka'idojin alakar kasa da kasa bisa tushen ka'idojin MDD, kana suna goyon bayan manufar kafa tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, tare kuma da kin amincewa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, ban da haka kuma suna goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa tushen ka'idojin da aka tsara. suna kuma ganin cewa, akwai bukatar yiwa kungiyar cinikayya ta duniya gyaran fuska da kuma kara aikinta da dai sauransu.

Gudanar da hakikanin hadin kai da cimma nasara tare, muhimmin karfi ne wajen zurfafa hadin kai a tsakanin Sin da EU. Yanzu bangarorin biyu na kokarin mayar da ra'ayin bai daya zuwa samun nasara tare, kana kuma suna kara nuna amincewa da juna a yayin da suke warware wasu matsaloli tare, hakan zai taimaka wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninsu. Ga misali, game da batun samar da iznin shiga kasuwa, firaminista Li ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen ketare, da kaddamar da sabbin manufofi da matakai, a waje guda kuma, za ta kara kyautata yanayin cinikayya, don saukaka hidima iri daya ga kamfanoni na Sin da na kasashen ketare. Baya ga haka, bangarorin Sin da EU sun amince da kafa yanayin cinikayya mai adalci tare, kamata ya yi bangarorin biyu su nuna wa juna ra'ayin rashin nuna bambanci ga kamfanoninsu. Ga misalin, game da batun zuba jari ga juna, yanzu yawan jari da EU ke zuba wa kasar Sin kashi 4 cikin dari ne kawai na jimilar jarin da take zubawa, kuma yawan jarin da kasar Sin ke zubawa EU kashi 2 cikin dari ne kawai na jimilar jarin da EU ke jawowa. Don haka, ana iya cewa, bangarorin biyu suna da makoma mai kyau a fannin zuba jari. Yanzu wasu sassa dake cikin yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da EU na gaggauta yin shawarwari kan aikin da suka shafi takardu da matakan da za su samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin bangarorin biyu wajen zuba jari ga juna, da kuma ba su kariya sosai a wannan fannin.

A shekarar da ta wuce, kasashen Turai sun fuskanci rashin kwanciyar hankali da kuma kalubaloli. Sabili da haka, wasu mambobin kungiyar EU suka nuna shakku da rashin fahimta ga kasar Sin. Kamar yadda firaministan kasar Sin ya ambato cikin bayaninsa da aka wallafa a jaridar Handelsblatt ta Jamus, wuraren da kasashen Sin da Turai suka sha bamban da juna, kuma haka lamari yake a tarihinsu, al'adunsu, tsarin zaman al'ummarsu da kuma hanyarsu ta raya kasa. Don haka suna da mabambantan ra'ayoyi da ma sabani kan wasu batutuwa. Sai dai a yayin da suka kuma hada kai a sassa daban daban, ba shakka za su gamu da matsala har ma da rikici. Amma sakamakon zurfafa fahimtar juna da kuma hadin gwiwa dake tsakaninsu, ya sa karin al'ummar Turai sun kara fahimtar cewa, hade shawarar "ziri daya da hanya daya" da kuma manufar EU ta nahiyoyin Turai da Asiya za ta samar da zarafi. Hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai ta bude kofa ga kowa, tana kuma taimakawa kyautata hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai.

Hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Turai na amun ci gaba, inda aka samu hakikanin sakamako tare da amfanawa jama'ar bangarorin 2. A fannin hadin gwiwar da ake yi bisa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", wasu kasashen kungiyar EU fiye da 10 sun riga sun kulla yarjejeniya tare da kasar Sin, cikinsu har da Hungary, da Poland, da Girka, da Portugal, da dai sauransu. Ban da haka, a kwanakin baya kasar Italiya ita ma ta shiga yarjejeniyar "Ziri Daya da Hanya Daya", wadda ita ce mamban kungiyar G7 ta farko da ta sa hannu kan yarjejeniyar. A nata bangare, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, ta bayyana a wajen taron kolin kungiyar EU da ya gudana a watan Maris na bana cewa, kasarta za ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Haka zalika, ta yi kira da a tabbatar da moriyar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki. Jaridar Handelsblatt ta kasar Jamus ta taba wallafa wani sharhi dake cewa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta baiwa nahiyar Turai damar samun ci gaba, kana ana ganin amfanin shawarar a zahiri. Ban da haka, cikin wani sharhi na daban da aka wallafa a jaridar Handelsblatt, an bayyana yiwuwar samun rashin fahimta kan niyyar kasar Sin a kasashen Turai, abun da zai sa a dauki matakai marasa dacewa. Idan hakan ya abku, a cewar sharhin jaridar, kasashen Turai za su rasa damarsu ta karshe ta taka muhimmiyar rawa a duniya a nan gaba.

Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar kara bude kofa ga kasashen waje, kana kasashen Turai suna da irin wannan manufa. Sin da Turai abokai ne na kwawai da suke yin kokarin samun zaman lafiya da kwanciyar lafiya da wadata a duniya. Sin da Turai sun zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kara bude kofa da yin hadin gwiwa, da fadada ayyukan samun moriyar juna, da raya tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa, da kuma shiga aikin tafiyar da harkokin duniya tare, matakan da za su amfanawa jama'ar Sin da Turai, da kuma tabbatar da tsarin duniya yadda ya kamata. (Lubabatu Lei, Kande Gao, Jamila Zhou, Bilkisu Xin, Bello Wang, Tasallah Yuan, Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China