in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar na ziyara a Amurka
2019-04-10 15:06:04 cri

Shugaba Donald Trump na Amurka ya tattauna da shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar dake ziyara a kasar ta Amurka, kan batutuwan da suka shafi tsaron shiyya da kuma ruwa.

Wata sanarwa da fadar shugaban Amurka ta White House ta fitar na cewa, a lokacin ziyarar ta Sisi, wadda ita ce ta biyu tun shekarar 2017, shugabannin biyu za kuma su tattauna kan halin da ake ciki a kasar Libya da barazanar kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslin Brotherhood.

Bugu da kari, Trump da Sisi za su tabo batutuwan da suka shafi ruwa, wadanda ke da muhimmanci ga kasashen biyu. Wadannan batutuwa masu sarkakiya, a cewar sanarwar, wajibi ne a magance su ta hanyar sasantawa tare da martaba dokokin kasa da kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China