in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da EU sun cimma matsaya kan ci gaba da yin shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari tsakanin bangarorin biyu
2019-04-10 14:45:12 cri

A yammacin jiya Talata ne, aka bayar da wata hadaddiyar sanarwa game da tattaunawar shugabannin Sin da EU karo na 21 bayan tattaunawar da aka shirya a Brussels a karkashin shugabancin firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar EU Donald Tusk, da kuma shugaban kwamitin EU Jean-Claude Juncher, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya kan ci gaba da yin shawarwari game da yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da EU a cikin wannan shekara, kana da cimma wata muhimmiyar yarjejeniya kafin shekarar 2020.

A yayin ganawar, firaminista Li ya bayyana cewa, ko da yaushe kasar Sin na mai da hankali kan Turai, tare da goyon bayan hanyar da kasashen Turai suka zabi ta neman dunkulewa, da kokarin zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni ta samun moriya da nasara tare a tsakaninta da EU. A cewar firaministan,

"Mun cimma matsayin daya, sakamakon yanayi mai sarkakiya da duniya ke ciki a halin yanzu, a matsayinsu na muhimman karfin kiyaye zaman lafiyar duniya, da inganta wadata da ci gaban duniya, ya kamata Sin da EU su hada kansu. Moriyar bai daya a tsakaninmu ta fi bambancin dake tsakaninmu, kara habaka moriyar bai daya zai taimaka wajen rage bambancin dake tsakaninmu, ta yadda jama'ar bangarorin biyu za su ci gajiya. "

Baya ga haka, Li Keqiang ya bayyana cewa, a yayin tattaunawar, bangarorin biyu suna ganin cewa, ya kamata su kiyaye ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da girmama dokokin kasa da kasa da ka'idojin dangantakar kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, kana da goyon bayan tsarin cinikayyar bangarori da dama bisa dokoki, karkashin jagorancin kungiyar WTO, da nuna adawa da ra'ayin ba da kariyar ga harkokin cinikayya. Ban da wannan kuma, sassan biyu, za su karfafa tattaunawa da hadin kai a tsakaninsu game da batun yiwa kungiyar WTO kwaskwarima. Li ya kara da cewa,

"Muna ganin cewa, kamata ya yi mu gaggauta yin shawarwari kan yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da EU, da nufin samun muhimman ci gaba kafin karshen shekarar da muke ciki, ta yadda za mu cimma wata muhimmiyar yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Sin da EU kafin karshen shekara mai zuwa, wadda za ta nuna adalci da bude kofa ga juna kan kamfanonin zuba jari na bangarorin biyu."

Bisa hadaddiyar sanarwar, bangarorin biyu sun kuma amince da kara inganta hadin kai karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", da ka'idojin EU game da hada kai da cudanya tsakanin Turai da Asiya, kana da karfafa hadin kai a fannonin sauyin yanayi, makamashi masu tsabta da dai sauransu.

Shugabannin EU sun bayyana cewa, bisa sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, EU tana son karfafa hadin kai da dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin. Kana kuma tana nuna yabo sosai kan jerin ra'ayoyin bai daya da bangarorin biyu suka cimma a yayin tattaunawar, a cewarsu, hadaddiyar sanarwar da suka bayar ta nuna wa duniya cewa, an kara samun sabon ci gaba kan dangantakar dake tsakanin Sin da EU. Shugaban kwamitin EU Jean-Claude Juncher ya bayyana cewa,

"Dangantakar abokantaka dake tsakaninmu, ta fi ta baya muhimmanci. Yanzu muna fuskantar kalubalen iri daya, a sa'i guda kuma gaba daya muna ganin cewa, hadin kai a tsakaninmu zai taimaka wa duniya wajen kara samun karfi da tsaro da kuma wadata."

Bayan tattaunawar da aka shirya a wannan rana, Li Keqiang da Donald Tusk da kuma Jean-Claude Juncher sun kalli yadda aka sanya hannu kan jerin takardun hadin kai a tsakanin Sin da EU a fannonin makamashi da takara da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China