in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta yi kira da a dauki matakan siyasa don magance matsalar 'yan gudun hijira
2019-04-10 10:59:54 cri

Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) Filippo Grandi, ya yi kira da a yi amfani da matakai na siyasa wajen magance matsalar da 'yan gudun hijira ke fuskanta a sassan duniya.

Grandi wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamitin sulhu na MDD, ya ce lokaci yana kurewa, duba da yadda 'yan gudun hijira da masu kaura ke fuskantar kyama, da gazawar tsoffin matakan da ake dauka game da halin da 'yan gudun hijirar ke ciki, abin da ke kara ta'azzara matsalar.

Ya ce, matakin siyasa zai inganta matakan warware wannan matsala, kamar yadda kunshe cikin sabon tsarin kula da 'yan gudun hijira na duniya da babban zauren MDD ya amince da shi a shekarar 2018, matakin da aka yi yakinin zai magance wadannan matsaloli, kuma kwamitin sulhun na da babbar rawa da zai taka.

Don haka, ya yi kira da a kara daukar matakai na samar da zaman lafiya da tsaro, da taimakawa kasashen dake karbar dimbin 'yan gudun hijira da kawar da abubuwan dake hana ruwa gudu kan magance wannan matsala, musamman mayar da mutane kasashensu na asali.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China