A jiya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, gwamnatinsa na shirin sanya rundunar sojojin kasar Iran ta IRG, cikin jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci. Hakan zai zama karo na farko da kasar Amurka ta sanya rundunar sojojin wata kasa cikin jerin sunayen.
Dangane da batun, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kamata ya yi a nuna biyayya ga ka'idojin huldar kasa da kasa, wadanda aka kafa su bisa tushen kundin tsarin mulkin MDD. Sa'an nan a magance daukar matakan nuna fin karfi, da bin ra'ayi na kashin dankali. (Bello Wang)