in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta sanya dakarun Amurka dake yammacin Asiya a matsayin kungiyar 'yan ta'adda
2019-04-09 09:24:21 cri

Rahotanni daga kasar Iran na cewa, majalisar kolin harkokin tsaron kasar, ta ayyana rundunar tsaron kasar Amurka dake yammacin Asiya a matsayin "kungiyar 'yan ta'adda".

Majalisar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, ta ce, tana daukar gwamnatin Amurkar a matsayin mai daukar nauyin ayyukan ta'addanci, ta kuma ayyana babbar rundunar Amurkar da dakarun dake kawance da ita a yammacin Asiya, a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Sanarwar ta kara da cewa, Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda Amurka ta ke kokarin sanya dakarun juyin-juya halin musulunci na Iran(IRGC) a matsayin kungiyar 'yan ta'addan ketare, matakin da Iran din ta bayyana a matsayin mai hadari wadda kuma ya saba doka.

A cewar sanarwar, matakan Amurka marasa hujja da nuna son kai kan dakarun na IRGC, za su gurgunta zaman lafiya da tsaro a shiyyar, da ma duniya baki daya. Kana hakan ya keta dokokin kasa da kasa da kudurin MDD.

A jiya ne, shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa, Amurka ta ayyana dakarun juyin-juya halin musulunci na Iran(IRGC) a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ta ketare, matakin da zai kara dagula alakar Amurka da Iran, da ma yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China