in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sanar da murabus din sakatariyar tsaron cikin gidan Amurka
2019-04-08 09:49:21 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a shafinsa na twitter a ranar Lahadi cewa sakatariyar tsaron cikin gidan kasar Kirstjen Nielsen zata sauka daga kan mukaminta.

Kwamishinan hukumar kwastam da tsaron kan iyakokin kasar na yanzu Kevin McAleenan shine zai rike sakataren hukumar na wucin gadi, Trump ya sake bayyana hakan a wani sakon twitter na daban.

Sai dai ba'a yi cikakken bayani game da musabbabin yin murabus din madam Nielsen ba. Amma wasu rahotannin gidan talabijin na CNN ya rawaito cewa, wani jami'in gwamnatin Amurkar ya nuna cewa Nielsen bata da kwarewar aiki na rike mukamin daidai da bukatar mista Trump.

Jaridar The New York Times ta labarto shugaba Trump ya nuna rashin jin dadinsa game da Nielsen sakamakon yadda aka samu karuwar 'yan cin rani dake shiga kasar ta Amurka wanda aka dora alhakin gazawarta ne wajen tabbatar da tsaron kan iyakokin kasar.

Nielsen, 'yar shekaru 46 a duniya, ta dare kan mukamin ne a ranar 6 ga watan Disambar shekarar 2017, bayan da mutumin data gada John Kelly ya samu karin girma zuwa matsayin babban jami'i a fadar White House.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China