in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraqi sun cafke mayakan IS yayin wani samame a gabashin Iraqi
2019-04-08 09:45:20 cri
Dakarun Iraqi sun kai hari kan maboya 3 na mayakan IS na sirri a lardin Diyala dake gabashin kasar, inda suka cafke 'yan kungiyar da dama, ciki har da wani fitaccen shugabansu.

Shugaban kwamitin tsaro na lardin Sadiq al-Husseini, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami'an hukumar tattara bayanan sirri ta Diyala tare da goyon bayan sojoji da 'yan sanda, sun kai samamen ne don farautar mayakan IS a yankuna daban daban na lardin.

Dakarun sun cafke mayakan IS, ciki har da wani fitaccen shugabansu, wanda ake ikirarin shi ne jigonsu a lardin.

Sadiq al-Husseini, wanda bai yi karin bayani game da dalilan da suka sabbaba samamen ba, ya ce jami'an tsaron sun yi ammana shugaban da suka cafke makusanci ne ga babban shugaban kungiyar IS, Abu Bakr al-Baghdadi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China