in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
G7: ba a daidaita sabanin dake tsakanin Palasdinu da Isra'ila ba
2019-04-07 16:23:10 cri

Jiya Asabar 6 ga wata, aka rufe taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G7 a birnin Dinard da ke arewa maso yammacin kasar Faransa. Kasashen 7 wato kasashen Faransa, Jamus, Japan, Canada, Amurka, Birtaniya da Italiya sun bayyana aniyarsu na inganta hadin gwiwa a fannonin yaki da ta'addanci, tabbatar da tsaro kan yanar gizo ta Intanet, kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka da dai sauransu, sai dai ba su cimma daidaito kan batun Palasdinu da Isra'ila da kuma yadda za su daidaita huldar dake tsakaninsu da kasar Iran ba.

A yayin taron manema labaru da aka yi bayan taron, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce, ministocin harkokin wajen Faransa, Jamus, Japan da Canada sun yi kira a kiyaye tare da farfado da ra'ayin kasancewar sassa daban daban na duniya domin daidaita batun sauyin yanayi da sauran batutuwan kasa da kasa, amma ba'a ambaci matsayin Amurka, Birtaniya da Italiya kan wannan batu ba.

A cikin sanarwar bayan taron da aka rabawa manema labaru, an ce, kasashen 7 sun tattauna rikicin da ke tsakanin Palasdinu da Isra'ila, wanda suke da sabani kansa. Ban da haka kuma, kasashen 7 ba su cimma ra'ayi daya kan yadda za su daidaita huldar dake tsakaninsu da Iran ba, a cewar Le Drian. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China