in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran Sin da Amurka za su kara taka rawa a cikin harkokin duniya
2019-04-06 16:48:05 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gana da Liu He, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firayin ministan kasar kuma jagoran bangaren kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka, wanda ke halartar tattaunawar manyan jami'an kasashen biyu karo na 9 a birnin Washington. Yayin ganawar da aka yi ranar Alhamis da ta gabata, Donald Trump ya ce, yana fatan tawagogin sassan biyu za su daddale yarjejeniya da wuri, saboda zai amfanawa kasashen biyu, da ma daukacin kasashen duniya. Kana yayin da yake amsa tambayar da mai yin sharhi kan harkokin duniya na babban rukunin gidajen rediyo da talebijin na kasar Sin CMG ya yi masa game da sauke nauyi a cikin harkokin duniya, shugaba Trump ya bayyana cewa, wannan batu ne mai muhimmanci ga kasashen Sin da Amurka.

An lura cewa, kafin wannan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin da Amurka suna sauke babban nauyin dake bisa wuyansu a bangaren ingiza zaman lafiya da wadata a fadin duniya, yanzu haka a cikin sakonsa da Liu He ya mikawa takwaransa na Amurka Donald Trump, Xi ya sake jaddada cewa, a halin yanzu idan ana gudanar da alakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin lumana, hakan zai amfanawa moriyar al'ummomin kasashen biyu, da kuma moriyar al'ummomin kasashen duniya baki daya. A don haka, idan ana son cimma burin, dole ne shugabannin kasashen biyu su kara mai da hankali kan batun. Yanzu abun da Trump ya fada game da sauke nauyi a cikin harkokin duniya, martani ne da ya mayar ga abun da Xi ya fada.

Hakika yanayin da kasashen duniya ke ciki na fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, shi ya sa kasashen duniya suke sa ran cewa, bisa matsayinsu na manyan kasashe mafiya kawo wa sauran kasashen duniya tasiri, kasar Sin da Amurka za su kara taka rawa a cikin harkokin duniya, musamman ma a fannoni uku:

Da farko, ya kamata su kara taka rawa a fannin samun ci gaba a fadin duniya. Yanzu ba samun ci gaban tattalin arzikin duniya kadai ake bukata ba, domin ana bukatar samun ci gaba mai daidaito, wanda zai amfanawa daukacin al'ummomin kasashen duniya baki daya, ta yadda za a rage ratar dake tsakanin masu wadata da matalauta. Kana bisa matsayinsu na manyan kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki a duniya, ya kamata kasar Sin da Amurka su kara sauke nauyin dake wuyansu a fannin samun ci gaban tattalin arizkin duniya. Amma a shekarar da ta gabata, kasashen nan biyu sun yi rigingimu a bangaren tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, lamarin da ya sa karuwar tattalin arzikin duniya ta gamu da matsala, har ta gaza samun ci gaba yadda ya kamata. A sakamakon haka, wasu hukumomin kasa da kasa sun rage hasashen da suka yi kan karuwar tattalin arzikin duniya a bana, misali hukumar cinikayya ta duniya ta rage hasashen daga kaso 3.7 bisa dari zuwa kaso 2.6 bisa dari, a karkashin yanayin, idan Sin da Amurka suka daddale yarjejeniyar cinikayya mai amfanawa juna, ko shakka babu zai sa kasashen duniya su cika da imani, haka kuma zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.

Na biyu, ya kamata su kara taka rawa a fannin shimfida zaman lafiya a fadin duniya. Yanzu bil Adama na fuskantar kalubaloli da dama, wasu yankuna na fama da tashe tashen hankali yayin da wasu kuma ke fama da hare-haren ta'addanci, inda dukka wadannan ke kawo barazana ga tsaron bil Adama. A don haka bisa matsayinsu na zaunannun kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD, ya dace kasar Sin da Amurka su ba da jagoranci kan aikin shimfida zaman lafiya a fadin duniya, ta yadda za a tabbatar da tabbaci da kuma zaman karko ga zaman lafiyar kasa da kasa. A kwanakin baya, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta hana amfani da maganin Fentanyl a kasar tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana. Yayin da yake ganawa da Liu He, Trump ya yabawa wannan kuduri na kasar Sin, saboda yana ganin cewa, matakin da ta dauka yana da babbar ma'ana ga hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren yaki da miyagun kwayoyi.

Na uku, ya kamata su kara taka rawa kan aikin gudanar da harkokin duniya. yanzu tsarin gudanar da harkokin duniya ya gamu da matsala, a don haka kasashe da dama sun gabatar da bukatar yin gyare-gyare kan tsarin, ana fatan kasashen duniya za su warware matsalar ta hanyar yin shawarwari.

Tsohon jami'in diplomasiyya na Amurka Nicolas Platt, ya bayyana cewa, dole ne kasar Sin da Amurka su daidaita alakar dake tsakaninsu cikin kwanciyar hankali, domin babu sauran zabi a gabansu, saboda hakan ne zai amfanawa moriyar al'ummomin kasashen biyu. Domin cimma wannan buri, ya dace kasashen biyu su kara taka rawa a cikin harkokin duniya ta hanyar daukar matakan da suka dace.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China