in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kamfanin Boeing ya amince da kuskuren tsarin sarrafa jirgi ne ya haddasa hadarin jiragen sama
2019-04-05 16:36:25 cri
A jiya ne, shugaban kamfanin Boeing na kasar Amurka Dennis Muilenburg ya wallafe wata sanarwa a shafin intarnet na kamfanin, inda ya amince cewa, kuskuren tsarin sarrafa jirgi a lokacin dake fuskanci matsala wato MCAS ne ya haddasa hadarin jiragen sama biyu mai samfurin 737 Max-8 a kwanakin baya, kana ya bayyana cewa, za a kyautata wannan tsari a cikin wasu makwanni masu zuwa.

A ranar 10 ga watan Maris, jirgin sama samfurin Boeing 737 Max-8 na kamfanin jiragen saman kasar Habasha ya fadi, wannan ne karo na biyu da jirgin saman Boeing ya yi hadarin bayan jirgin saman Boeing na kamfanin Lion Air na kasar Indonesia ya fadi a ranar 29 ga watan Oktoba na bara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China