in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taya Azali murnar sake zabarsa a matsayin shugaban Comoros
2019-04-03 20:51:51 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya shaidawa taron manema labarai cewa, kasarsa na taya Azali Assoumani murnar sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban Comoros.

Geng Shuang ya ce, Sin da Comoros na jin dadin dadadden zumuncin dake tsakaninsu, kuma bangaren Sin yana dora muhimmanci kan raya alakar dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, a shirye Sin take ta yi aiki da sabuwar gwamnatin Comoros wajen karfafa dangantakar abokantaka a fannonin daban-daban karkashin laimar dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da dandalin alakar Sin da kasashen Larabawa don ciyar da hadin gwiwar abokantaka tsakanin kasashen biyu zuwa babban mataki.

A jiya Talata ne, kotun kolin kasar Comoros ta sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar na karshe, inda ta tabbatar da sake zabar Azali a matsayin shugaban tsibirin kasar dake tekun Indiya, inda ya samu kaso 59.05 na kuri'un da aka kada,(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China