Ma Zhaoxu, ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin sulhu na MDD dake goyon bayan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, gabanin taron bitar da za a yi a 2020.
Wakilin na Sin, ya ce ya kamata kasashen su daina amfani da dabarun kare kai da makaman nukiliya ta hanyar kai harin ba-zata, sannan su soke rawar da makaman ke takawa cikin dabarunsu na tsaron kasa.
Ya ce kasar Sin na kira musammam ga Rasha da Amurka, su ci gaba da warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa, tare da komawa ga kiyaye tanade-tanaden yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango nan bada dadewa ba, sannan su lalubo hanyar tsawaita yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya dake tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)