in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da damar cinikayya maras shinge cikin yarjejeniyar hada hadar ta da Koriya ta kudu
2019-04-03 09:44:13 cri
Ma'aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce mahukuntan kasar sun amince da shigar da damar cinikayya maras shinge, cikin yarjejeniyar hada hadar Sin da Koriya ta kudu.

Hakan dai na nufin kasashen biyu na da damar shigar da daukacin hajojin cinikayya, da ayyukan ba da hidima na kasashen juna ba tare da wani tarnaki ba. Wannan ne dai karon farko da Sin ta gabatar da wannan batu, yayin tattaunawar sassan biyu game da batutuwan da suka shafi cinikayya cikin 'yanci, da harkokin ba da hidima, da ma batun zuba jari tsakanin sassan biyu.

An kuma gabatar da shawarar ne yayin zagaye na hudu na tattaunawar sassan a karo na biyu da ta gudana a 'yan kwanaki a nan birnin Beijing. Burin wannan manufa dai shi ne saukaka ayyukan ba da hidima, da cinikayya, da inganta muhallin zuba jari tsakanin kasashen biyu.

An fara aiwatar da yarjejeniyar cinikayya tsakanin Sin da Koriya ta kudu ko "Sino-Korea FTA" ne, tun daga watan Disambar shekarar 2015, kana aka fara aiwatar da zagaye na biyu na yarjejeniyar daga watan Disambar shekarar 2017.

Daga shekarar 2015 kawo yanzu, kasashen biyu sun ragewa juna haraji har karo hudu, baya ga wasu yarjeniyoyin cinikayya da aka daukewa harajin gaba daya, wadanda kuma suka kai kaso 50 bisa dari na jimillar yarjeniyoyin da sassan biyu suka kulla.

Sin ce babbar abokiyar cinikayya Koriya ta kudu mafi girma a fannin fitar da kayayyaki da shigo da hajoji, yayin da Koriyar ke matsayi na uku a jerin kasashe mafiya gudanar da hada hadar cinikayya da Sin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China