in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ya taimaka ga ci gaban Beijing mai inganci
2019-04-02 19:39:23 cri

A cikin shekarun baya bayan nan, birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ya shiga mataki na samun ci gaba mai inganci, wato ya fi mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ake samarwa ta hanyar yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a birnin, a maimakon karuwan adadinsu kawai.

Kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII na Beijing yana yankin Zhongguancun na birnin Beijing, an kuma kafa shi ne a shekarar 2011, ya zuwa shekarar 2018, an zabe shi a matsayin daya daga cikin fitattun kamfanonin dake kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a bangaren hotunan bidiyo goma a fadin duniya, ayyukan da kamfanin ke gudanarwa sun kunshi fasahar tantance hoton fuska, da fasahar tantance hotun jikin mutum, da fasahar tantance hoton alamar hannu, da fasahar tantance takardar shaida, da fasahar tantance hotuna daban daban.

Mataimakin shugaban kamfanin Xie Yinan ya yi mana bayani cewa, tun farkon kafuwar kamfaninsa, sun yi kokari matuka domin nuna fifikonsu inda suka yi amfani da fasahar zamani a bakin kofar kamfanin, misali sun kera na'urar tantance hoton fuska a bakin kofa, saboda a wancan lokaci, yana da wahala a yi amfani da fasahar, yanzu haka suna amfani da fasahar samar da bidiyon komai da ruwanka (IOT) wato Internet of Things, ta zamani.

Irin wannan fasaha tana da amfani sosai, misali ana iya samar da cikakkun bayanai kan kayayyakin da ake bukata ta hanyar samar da hoto da murya da sauransu, mataimakin shugaban kamfanin Xie Yinan ya bayyana cewa, idan ana amfani da na'urar a cikin kasuwa mai fadin muraba'in mita dari uku ko hudu, ana iya gano wane ne ya karbi wane irin kaya a wane lokaci, bisa tushen, za a iya gano cewa, wane irin kaya ya fi samun karbuwa a wajen masu sayayya.

Hakika ma'aikatan kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII suna ganin cewa, yin amfani da fasahar AI ba domin maye gurbin mutane ba ne, sai domin kara kyautata ayyukan da ake gudanarwa, makasudin kwaikwayon tunanin dan Adam, (AI) shi ne domin kara saukaka aikin mutane da kuma harkokin rayuwa, tare kuma da samar da alheri ga daukacin bil Adama.

Mataimakin shugaban kamfanin Xie Yinan yana ganin cewa, ainihin ma'anar yin kirkire-kirkire ita ce kyautata sana'o'i da kuma rage kudin da aka kashe kan su.

A yankin Zhongguancun, kamfanonin da suka yi kama da kamfanin kimiyya da fasaha na Kuangshi wato MEGVII suna da yawan gaske, a shekarar 2018, adadinsu ya kai sama da dubu 22, kwatankwacin adadin kudin shigarsu ya kai kudin Sin yuan biliyan 5800, adadin da ya karu da kaso 11 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin shekarar 2017.

Ya zuwa shekarar 2018, adadin kamfanonin kimiyya da fasahar zamani na birnin Beijing ya kai dubu 25, adadin da ya karu da kaso 25 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2017, adadin kamfanonin Unicom wato darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 1 a birnin ya kai 80, wato ko wace rana adadin sabbin kamfanonin kimiyya da fasahar zamani da aka kafa a birnin ya kai 199, kana adadin kwangilar fasahar da aka daddale shi ma ya karu da kaso 10.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017.

Hakazalika, ya zuwa karshen 2018, adadin 'yancin mallakar fasaha na mazauna birnin Beijing dubu goma ya kai 111.2, kuma adadin bukatar rokon neman samun 'yancin mallakar fasaha da aka gabatar a birnin ya karu da kaso 13.6 bisa dari kuma adadin 'yancin mallakar fasahar da aka samu ya karu da kaso 15.47 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2017.

A bayyane an lura cewa, ci gaban Beijing mai inganci yana da makoma mai haske.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China