in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu bukatar kasashen Turai su damu kan ci gaban kasar Sin
2019-04-02 17:01:55 cri

Shugaban hadaddiyar kungiyar BGA ta Jamus Holger Bingmann ya bayyana cewa, "Bai kamata ba hankalinmu ya tashi, a halin da ake ciki yanzu babu bukatar a nuna damuwa kan ci gaban kasar Sin", kana ya kara da cewa, "A koda yaushe kada kasashen Turai su sanya katanga yayin gudanar da harkokin cinikayya."

Wannan kashedi ne da ya yi kan damuwar da ake nunawa kan ci gaban kasar Sin da sauyawar manufar raya masana'antun kasashen Turai.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters na Birtaniya ya bayar da wani labari cewa, a kwanakin baya bayan nan, kasashen Jamus da Faransa sun gabatar da shawara cewa, ya kamata gwamnatoci su kara taka rawa yayin da take aiwatar da manufar raya masana'antu a kasashen, haka kuma suna fatan za su kara habaka ci gaban kamfanoni a kasashen, ta yadda za su yi gogayya da kamfanonin kasar Sin da na Amurka.

Game da batun, Holger Bingmann ya yi gargadin kada a ji tsoron kasar Sin a tafiyar da manufar rufe kofarsa.

A kwanan baya, kasar Italiya da kasar Sin sun rattaba hannu kan takardar bayani bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", bisa aniyar hada kan kasashen biyu wajen ci gaba tare. Dalilin da ya sa Italiya ta yi hakan shi ne domin jawo jari daga kasar Sin wajen raya muhimman ababen more rayuwarta, da sa ran sayar da kayayyakinta a kasuwar Sin da sauran kasashen da shawarar ta shafa. Amma wannan lamarin ya damu wasu 'yan kasashen Turai, har ma sun nuna rashin jin dadinsu. Alal misali, suna ganin cewa, hadin kan Sin da Italiya ya sa Turai ta rabu, kuma sun nuna damuwa kan cewa, yadda kasar Sin ta zuba jari a kungiyar EU zai sa tattalin arzikin kasar Sin ya kara bada tasiri ga kungiyar.

A hakika dai, idan aka duba wannan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, watakila za a canja ra'ayi. A karkashin yanayin da ake ciki a yanzu, Sin da Turai su ne abokan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare kan manyan batutuwan duniya da dama. Alal misali, bayan da kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar Paris, Sin da Turai sun bada jagoranci ga ci gaba da yin kokarin tinkarar sauyin yanayi a tsakanin kasa da kasa. Bayan da kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliya ta Iran, Sin da Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Rasha sun ci gaba da bin yarjejeniyar. Kungiyar EU ta kafa tsarin biyan kudi na musamman ga kasar Iran, kana kasar Sin ta nuna goyon baya sosai ga wannan batu. Game da tabbatar da tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban na duniya, Sin da Turai suna da ra'ayi daya ko kusan daya. Ana iya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Turai ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da doka da oda a duniya bisa tushen bin ka'idoji.

A labarin da kafofin yada labarai na kasar Jamus suka bayar, an ce, a bara, yawan kayayyakin da kamfanonin kasar suka fitar zuwa kasar Sin ya zarce Euro biliyan 93, a yayin da adadin kayayyakin da Faransa ta fitar zuwa kasar Sin ya kai kudin Euro biliyan 19, kuma adadin ya kai biliyan 19 ga kasar Italiya. Dalili ke nan da ya sa kasar Italiya ta yanke shawarar shiga shawarar "ziri daya da hanya daya", wato domin neman bunkasa tattalin arzikin kasar. Idan kungiyar tarayyar Turai ta dauki kwararan matakai a kan lokaci game da shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, lalle, ba wanda zai nuna damuwa game da yadda kasar Italiya ta shiga shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya".

Ba za a iya musunta haka ba, bisa ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, ba shakka za a rage gibin dake tsakaninta da kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen EU. Ko kasar Sin mai wadata ta cancanci a ji tsoronta? A hakika dai ba haka lamarin yake ba, kamar yadda Holger Bingmann ya fada a yayin zantawa da kafofin watsa labaru na kasar Jamus, ya ce, kason da wasu kamfanonin kasar Jamus suka samu a kan cinikayyarsu a kasar Sin ya riga ya wuce kashi 40 cikin dari. Holger Bingmann ya jaddada cewa, kasar Jamus ba wadda ta samu hasara ba ne, a maimakon haka tana daya daga cikin masu cin gajiya daga wajen tasowar tattalin arzikin kasar ta Sin.

A Juma'ar da ta gabata, aka kafa majalisar tarayyar Jamus game da shawarar "Ziri daya da hanya daya", wato BVDSI a takaice. A ganin majalisar, sai idan an sa himman wajen bin shawarar ne kawai, kasar Jamus za ta iya samun moriya. Shugaban majalisar kula da harkokin kamfanonin da iyali daya ke gudanarwa na Bremen Peter Bollhagen ya bayyana a yayin bikin kafa majalisar cewa, "kamata ya yi kamfanoni matsakaita da kanana na kasar Jamus su nuna kwarin gwiwa don sa himma wajen shiga ayyukan sabon tsarin na sabuwar hanyar siliki, wannan dama ce da ya zama dole ne mu kama." Ko shakka babu, wannan hanya ce mai tabbaci da ya kamata a bi ta. (Jamila, Kande, Lubabatu, Zainab, Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China