in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son kara ba da gudummawarta wajen samar da wuta da makamashin nukiliya
2019-04-02 14:14:37 cri




An gudanar da taron dandalin tattaunawar samar da makamashin nukiliya mai dorewa,jiya Litinin a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, inda masu ruwa da tsaki a fannin makamashin nukiliya da suka halarci taron daga ciki da wajen kasar suka tattauna kan bunkasa aikin samar da makamashin nukiliya da kuma kirkire-kirkire da hadin gwiwa a wannan fannin.

A yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauye a fannin tsarin makamashin duniya, kasashen duniya na kokarin bunkasa makamashi masu tsabta, kuma kowa na fatan kada a bar shi a baya.

A nan kasar Sin, a kokarin da aka yi cikin shekaru 30 da suka gabata, an kai ga wani babban mataki a fannin samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya. A gun taron da aka gudanar a wannan rana, Liu Baohua, mataimakin shugaban hukumar makamashi ta kasar Sin ya bayyana cewa, a bara, kasar Sin ta fara aiki da wasu jerin injuna bakwai, matakin da ya sa jerin injunan samar da wuta da makamashin nukiliya da ke aiki a kasar Sin ya kai 45, wadanda kuma ke iya samar da wutar lantarki da ta kai KW miliyan 45.9, abin da ya sa kasar ta zama ta uku a duniya. Ya ce,"Jerin sabbin injuna da aka fara aiki da su sun samar da kuzari ga bunkasuwar makamashi a kasar Sin. Baya ga haka, yadda ake aiki da wadannan injunan samar da wuta da makamashin nukiliya a kasar Sin, suna da muhimmiyar ma'ana ga bunkasuwar aikin samar da wuta da makamashin nukiliya a duk fadin duniya. Yanzu haka, wadannan injuna na aiki yadda ya kamata, kuma wutar lantarki da suke samarwa na karuwa cikin sauri, wadda ta karu da kaso 18.6% bisa makamancin lokacin a bara."

Har zuwa yanzu, babban aikin da kasar Sin ta sanya gaba shi ne bunkasa makamashi masu tsabta da suka hada da samar da wuta da makamashin nukiliya. A game da wannan, shugaban hukumar kula da tsaron nukiliya ta kasar Sin ya jaddada cewa, ya zama dole a tabbatar da tsaro a yayin da ake samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya.

 

A kokarin da kasar Sin ta yi cikin shekaru 30 da suka wuce, yanzu masana'antun samar da wuta da makamashin nukiliya na kasar na da kwarewar tsara fasalin injunan samar da wuta da makamashin nukiliya, kuma ta samu dimbin fasahohi ta wannan fanni. Don haka, a yayin da kasar Sin ke neman ci gaban kanta, tana kuma kokarin inganta hadin gwiwarta da kasa da kasa a fannin samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya. A jawabin da ya gabatar ta hoton bidiyo a gun taron da aka yi a wannan rana, babban darektan sashen kula da makamashin nukiliya na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, Mr. William Magwood ya bayyana cewa, an kai wani matsayin da ba a taba gani ba a hadin gwiwar da ake yi da kasar Sin. Ya ce,"Domin tinkarar kalubale na bai daya da ake fuskanta, kasar Sin na kara hadin gwiwa da sashenmu. Kasar Sin babbar abokiyar hadin gwiwa ce gare mu, kuma alakar da ke tsakaninmu tana ta habaka. Ina alfahari da cewa, ta fannin hadin gwiwar makamashin nukiliya, Sin da sashenmu na taimakon juna bisa kwarewar kowanenmu, kuma mun kai wani matsayin da ba a taba gani ba a wajen hadin gwiwar."

A nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin, Zhang Jianhua ya bayyana cewa, kasar Sin za ta tsaya ga bude kofarta, za ta kuma ci gaba gudanar da hadin gwiwa da kasa da kasa, don samun moriyar juna ta fannin bunkasa makamashin nukiliya. Ya ce,"Na farko, za mu ci gaba da bude kofar masana'antun samar da wuta da makamashin nukiliya ga kasashen ketare, mu ci gaba da yin hadin gwiwa da kasa da kasa bisa ka'idar cin moriyar juna. Na biyu, za mu yi kokarin sa kaimi masana'antunmu su bunkasa kasuwannin duniya, don su yayata fasahohi da injunan da muka kirkiro da kanmu, kuma su samar da taimako ga kasashen da ke kokarin bunkasa makamashin nukiliya. Na uku kuwa, za mu yi kokarin sa ido a kan kamfanoninmu da suke gudanar da harkokinsu a kasashen waje, don samar da yanayi mai kyau ga inganta hadin gwiwarmu da kasashen duniya ta fannin bunkasa masana'antun samar da makamashin nukiliya." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China