Mambobin sun kada kuri'ar da ta ki amnicewa da dukkan kudrori 4 na ficewar kasar daga EU, wadanda shugaban majalisar John Bercow ya zabo, a wani yunkuri na warware takkaddamar da ake yi game da batun ficewar kasar daga Tarayyar Turai. Gwamnatin Birtaniya dai na da nan zuwa 12 ga watan Afrilu domin ta yanke shawarar barin Tarayyar.
Mambobin majalisar sun kada kuri'un amincewa 261 da na kin amincewa 282, wanda ya nuna cewa ba a amince da kudurin Birtaniya na kasancewa cikin kasuwa daya da tarayyar Turai ba, da kuma yarjejeniyar haraji na bai daya da tarayyar.
Kudurin na amfani da haraji na bai daya na kasashen da suka amince da manufar, na nufin Birtaniya za ta ci gaba da dangantakar cinikayya ta kut-da-kut da Tarayyar Turai bayan ficewarta. (Fa'iza Mustapha)