Yayin wata muhawara kan dokokin agajin jin kai na kasa da kasa da kwamitin sulhu na MDD ya yi, Ma Zhaoxu, ya yi kira ga kasashe su kiyaye manufofi da ka'idojin MDD tare da dokokin ayyukan jin kai.
Ya ce ya kamata dukkan hukumomin agaji su kiyaye dokokin bada agaji na kasa da kasa da sauran dokokin masu alaka, tare da kaurecwa amfani da kai agajin jin kai domin siyasa ko aikin soji ko kuma wasu manufofi.
Ya kuma bukaci a hada hannu wajen warware rikice-rikice cikin lumana, wanda zai kai ga shawo kan matsalolin kare fararen hula tun daga tushe. (Fa'iza Mustapha)