in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban mamban majalisar kolin Sin ya bada shawarar bibiyar aikin yaki da fatara
2019-04-02 10:31:53 cri
Wang Yang, babban mamban hukumar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, ya bukaci jam'iyyun siyasa wadanda ba kwaminis ba da su kara sanya ido ga shirin yaki da fatara, ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da ya gudana a ranar Litinin.

A shekarar da ta gabata, kwamitin tsakiya na jam'iyyun da ba kwaminis ba sun kaddamar da wasu sauye-sauye game da shirin yaki da fatara kuma an cimma kyakkyawan sakamako, in ji Wang, mamban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin.

Ya kuma bukace su da su taimaka wajen sa kaimi, da nuna amincewa, kana su yi amfani da basirarsu da hikimarsu da arzikinsu wajen samar da kayayyakin tallafin da ake bukata a shirin yaki da fatara.

Ya kamata kananan kwamitoci na cikin gida da gwamnatoci su bada taimako tare da yin hadin gwiwa da jam'iyyun da ba kwaminis ba wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu na sanya ido kan shirin yaki da fatara, in ji mista Wang. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China