in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Liu He ya tashi zuwa Amurka don halartar tattaunawar ciniki karo na 9
2019-04-01 19:18:53 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, mataimakin firayin ministan kasar Liu He ya tashi zuwa Amurka domin halartar taron tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Amurka karo na 9.

Jami'in ya kara da cewa, kasarsa tana fatan sassan biyu za su yi kokari tare domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a kasar Argentina don darawa kan ci gaban da suka samu a halin yanzu, haka kuma yana sa ran za su daddale wata yarjejeniya mai amfanawa juna.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China