in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar ba da agaji ta kasar Sin ta kaddamar da aikin kashe kwayoyin cuta a kasar Mozambique
2019-04-01 13:17:42 cri


Kawo yanzu, kungiyar ba da agaji ta kasar Sin ta riga ta kaddamar da aikin ceto har na tsawon mako guda a yankunan da ke fama da ibtila'in guguwar Idai a kasar Mozambique. Ban da aikin ceto da ba da agajin jinya, 'yan kungiyar su ma sun gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta da rigakafin abkuwar annoba a wuraren da suka fi samun yawan mutane musamman ma matsugunan masu fama da ibtila'in. A halin yanzu dai, an riga an gano wadanda suka kamu da cutar kwalara a wasu wurare, adadin wadanda suka kamu da cutar gudawa ma yana ta karuwa. Don haka aikin kashe kwayoyin cuta da kungiyar ba da agaji ta Sin ta gudanar na da muhimmiyar ma'ana wajen rigakafin abkuwar cututuka masu yaduwa.

A wani wurin tsugunar da wadanda bala'in guguwar Idai ya shafa mai suna Ifaba, ma'aikatan jinya da kashe kwayoyin cuta na kungiyar ba da agaji ta kasar Sin suna shan hasken rana mai zafi, inda kuma suke gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta da kiwon lafiya a tantunan tsugunar da wadanda bala'in ya aukawa da ma sauran wuraren zamansu.

Georgina Fretto, mai kula da wannan matsugunin na Ifaba ta bayyana cewa, akwai mutane fiye da 1100 a matsugunin a halin yanzu, a ciki, akwai kimanin 900 da suka fito daga yankin Buzi da Ibtila'in guguwar ya fi shafa, sauran 200 kuma sun fito ne daga sauran wuraren da ke kusa da yankin Beira. Yanzu ana iya ba da tabbacin samar da isassun abinci ga matsugunin, likitocin kasar Mozambique ma na samar da aikin jiyya, amma kafin zuwan kungiyar ba da agaji ta kasar Sin, ba a taba gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta ba. Madam Georgina tana ganin cewa, ya zama wajibi a gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta da rigakafin abkuwar annoba a matsugunan da suka fi samun yawan masu fama da bala'in. Tana mai cewa,

"Muna bukatar a kashe kwayoyin cuta a wurin nan, ganin yadda ake samun sauro da yawa. Kawo yanzu dai, babu wanda ya zo ya kashe kwayoyin cuta."

Beatriz Garimbo tana daga yankin Buzi da ya fi fama da bala'in, wadda mijinta da surukanta dukka sun mutu sakamakon bala'in. An cece ta da diyarta ne bayan da suka zauna a kan wata bishiya har na tsawon kwanaki hudu ba tare da ci ko shan komai ba. Yanzu an tsugunar da su a wannan wurin, a cikin wani tantin da fadinsa ya kai kimanin murabba'in mita uku. Beatriz tana godiya ga aikin kashe kwayoyin cuta da kungiyar agajin kasar Sin ta yi. Ta kara da cewa,

"Mun gode da taimakon da kungiyar agajin kasar Sin ta ba mu. Aikin kashe kwayoyin cuta da suka yi na iya rigakafin kamuwa da wasu cututuka, lamarin da ke da muhimmanci sosai gare mu mazauna cikin tantuna."

Fan Chaoyun, shugabar reshen kungiyar agajin kasar Sin mai kula da aikin kashe kwayoyin cuta kuma kwararriya a wannan fanni, ta bayyana cewa, matsugunin na da mutane da yawa, yanayin kiwon lafiya ma ba shi kyau, don haka suna bada muhimmanci ga kashe kwayoyin cuta da ke kan kayayyakin da ke wurin da ma iskar da ke cikin tantuna. Ta ce,

"bayan shigarmu matsugunin, mun gano cewa, lallai akwai mutane masu dimbin yawa, da sharar da suka rube a ko ina. Ban daki ma na da dauda sosai, don haka mun kashe kwayoyin cuta a wuraren nan, bisa aniyar rage kiwon kwayoyin cuta, da katse hanyar yada cuta ta hanyar rage kiwon sauro da kudaje. Akwai yara da yawa da ke zama a nan, wadanda ba su da karfin kare jiki sosai. Idan ba ma son ganin abkuwar annoba mai tsanani bayan iftila'in, to kiyaye tsabtar muhalli da kashe kwayoyin cuta na da muhimmanci sosai."

A halin yanzu dai, an riga an gano wadanda suka kamu da cutar kwalara a yankin Beira da sauran wuraren da ke makwabtaka da shi. Adadin wadanda ke kamuwa da cutar gudawa ma na karuwa. Albert Muanido, wani kwararre kan kiwon lafiyar jama'a a Mozambique, yana ganin cewa, a wannan yanayin da ake ciki, aikin kashe kwayoyin cuta zai taimaka wajen kiyaye wani muhalli mai tsabta a matsugunan. Ya ce,

"Ina zaton cewa, muna bukatar irin wannan aikin na kashe kwayoyin cuta sosai, wanda zai taimaka wajen hana yaduwar cutar kwalara da gudawa. Yanzu ba a gano wanda ya kamu da kwalara a matsugunin ba tukuna, amma rigakafi ya fi magani, aikin kashe kwayoyin cuta zai rage illar da cutar gudawa ke yi wa matsugunin."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China