in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a yi babban taron tsara fasalin masana'antu na duniya na shekara ta 2019 a kasar Sin
2019-03-31 17:19:47 cri
Kwamitin shirya babban taron tsara fasalin masana'antu na kasa da kasa ya sanar kwanan baya a birnin Vienna cewa, za'a yi babban taron tsara fasalin masana'antu na kasa da kasa na shekara ta 2019, wanda kuma shine bikin baje-kolin sana'o'in tsara fasali na duniya a watan Oktobar bana a birnin Yantai na lardin Shandong dake arewacin kasar Sin.

Kungiyar tsara fasalin masana'antu ta kasar Sin gami da wasu kungiyoyin tsara fasali da hukumomi da kamfanoni gami da jami'o'i daga kasashe da yankuna sama da 30 a duk fadin duniya ne suka bada shawarar kira babban taron tsara fasalin masana'antu na duniya, da nufin taimakawa kirkire-kirkiren ayyukan tsara fasali da bunkasa tattalin arziki gami da kyautata zamantakewar al'umma.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China