in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi: Zan bautawa jama'a ba tare da la'akari da moriyar kaina ba
2019-03-28 10:48:51 cri

Ranar 22 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Robert Fico, shugaban majalisar wakilan kasar Italiya a birnin Rome na kasar, inda ya bayyana cewa, nan gaba zai ci gaba da bautawa al'ummomin kasarsa ba tare da la'akari da moriyar kansa ba, abun da shugaba Xi ya fada ya samu babban yabo daga wajen Sinawa, musamman Sinawan da suke amfani da yanar gizo.

Yayin ganawar sa da shugaban majalisar wakilan Italiya a Rome, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa: "Kasar Sin babbar kasa ce a duniya, a don haka ina sauke babban nauyi dake wuyana, haka kuma ina kullum ina fama da ayyuka masu yawan gaske, domin kara kyautata aikina a matsayin shugaban kasar, nan gaba zan ci gaba da yin kokari matuka domin bautawa al'ummomin kasata ba tare da la'akari da moriyar kaina ba, wato zan sadaukar da duk tsawon rayuwata don ganin ci gaban kasar ta Sin."

Abun da shugaba Xi ya fada ya burge mu matuka, hakika ya nuna mana cewa, shugaba Xi shugaban al'ummomin kasar Sin ne, a ko da yaushe yana mai da hankali kan muradun kasa da al'ummomin kasar.

A cikin wani littafi da Zhuang Zhou, wani shahararren mai zurfin tunani na zamanin Zhanguo a tarihin kasar Sin, ya rubuta game da sauye-sauyen da suka faru a duniyarmu, ya bayyana cewa, bai kamata mutum ya kula da moriyar kansa ba, saboda wannan shi ne babban imanin da ake da shi, idan mutum yana son samun karin iko ko kayayyaki, to hankalinsa zai gushe, amma idan mutum ya fi ba da muhimmanci kan moriyar kasa da ta jama'a, to ba zai damu da moriyar kansa ba, haka kuma zai sa ya bautawa jama'ar kasarsa ba tare da la'akari da moriyar kansa ba.

A bayyane ne ana iya fahimtar ma'anar kalaman da mai zurfin tunani Zhuang Zhou ya fada daga aikin shugaba Xi yayin da yake kokarin bautawa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da al'ummomin kasar ta Sin.

Misali shugaba Xi yana kokari matuka domin kara zurfafa yin gyare-gyare a gida, haka kuma yana yin iyakacin kokari domin yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar, kana yana sa kaimi kan aikin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama a fadin duniya, duk wadannan sun nuna mana babban sakamakon da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ke karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping ya samu a fannonin gudanar da harkokin jam'iyyar da harkokin kasar da kuma harkokin rundunar sojojin kasar, da kyautata tsarin kasar Sin da kuma tsarin tafiyar da harkokin duniya, da ingiza gyare-gyare da ci gaban kasa, tun bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar karo na 18 a shekarar 2012.

Bautawa jama'a imani ne da ya kamata ake da shi, a baya shugaba Xi ya taba bayyana cewa: "Burin mu shi ne, sama wa al'ummomin kasa kyakkyawar makoma."

Kana ya jaddada cewa: "Yanzu haka muna sauke nauyin dake wuyanmu na raya jam'iyyar JKS da kasar ta Sin, ya zama wajibi mu kara kokari matuka kan wannan aikin."

A daukacin wuraren da shugaba Xi ya taba yin aiki, bai taba mantawa da jama'ar kasarsa ba, har kullum yana mai da hankali kan rayuwarsu na yau da kullum, an lura cewa, a ko da yaushe shugaba Xi yana ba da muhimmanci ga moriyar kasa da ta jama'ar kasa, hakan ya nuna cewa, Xi shugaban kasa ne mai kishin jama'a matuka.

Idan mutum yana da imani, ko shakka babu zai cimma burinsa, shugaba Xi ya taba ba da misali cewa, "Da farko dai, 'dan wasan daukan kayan nauyi yana iya daukan kayan nauyin kilo 50 kawai, amma bayan ya samu horo, zai iya daukan kaya mai nauyin kilo 250. Lamarin da ya shaida cewa, idan na yi kokari tare da daukacin al'ummomin kasarmu da yawansu ya kai sama da biliyan 1 da miliyan 300, tabbas za mu samu makoma mai kyau, ina cike da imani kan wannan, al'ummomin kasar Sin su ma suna cike da wannan imani."

Maganar shugaba Xi ta kara karfafa gwiwar Sinawa, har suna yin alfahari cewa, abun alheri ne gare su saboda suna kokarin raya kasa karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping., haka kuma suna cike da imani cewa, ko shakka babu za su cimma burinsu na farfado da kasarsu daga duk fannoni karkashin jagorancin Xi bisa tushen hada kan al'ummomin kasar ta Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China