'Yan majalisar 441 sun yi galaba kan takwarorin 105 a zauren majalisar wajen gabatar da sabuwar ranar yarjejeniyar ficewar kasar, kana sun yi watsi da ainihin ranar da aka tsara Birtaniyan zata fice daga tarayyar Turai wato 29 ga watan Maris.
Tun da farko a ranar Laraba, May ta shedawa 'yan majalisar dokoki kasar cewa zata sauka daga matsayinta na firaiministar idan 'yan majalisar dokokin kasar suka goyi bayan bukatar data gabatar musu, wanda suka yi fatali da ita har sau biyu tun daga watan Janairu.
A bukatar data gabatawar 'yan majalisar dokokin bangaren Tory na neman amincewarsu ga bukatar data mikawa majalisar dokokin game da yarjejeniayar ficewar kasar, firaiministar tace, a shirye take ta sauka daga kan kujerarta tun ma gabanin lokacin da ta shirya yin murabus din. (Ahmad Fagam)