in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da dabarun warware "matsaloli 4" kan tafiyar da harkokin kasa da kasa
2019-03-27 17:33:24 cri

A yayin bikin rufe taron tattaunawar tafiyar da harkokin kasa da kasa da kasashen Sin da Faransa suka shirya tare a Paris a jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da wani jawabi mai take "A ba da gudummawa don raya kyakkyawar duniyarmu", inda bisa matsayin bunkasa al'ummomin bil Adama gaba daya, shugaba Xi Jinping ya bayar da dabarun kasar Sin kan yadda za a iya "kawar da matsalar rashin nagartaccen mulki bisa ka'idojin nuna adalci kamar yadda ya kamata. Sannan ya kamata a kawar da matsalar rashin amincewar juna bisa ka'idojin tattaunawa da kuma hakuri da juna. Bugu da kari, a kawar da matsalar rashin zaman lafiya ta hanyar tinkarar rikice-rikice cikin hadin gwiwa. Daga karshe, ya kamata a kawar da matsalar rashin ci gaba ta fannin moriyar juna da kuma neman nasara tare."

Yanzu duniya na fuskatar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari daya da suka gabata, misali kasashe masu saurin ci gaban tattalin aziki da kasashe masu tasowa sun yalwatu matuka, inda adadin karuwar tattalin arzikin da suka samu ya kai kaso 80 bisa dari daga cikin daukacin adadin karuwar tattalin arzikin kasashen duniya baki daya, wannan na nuna cewa, kusan an cimma burin samun ci gaban bangarori daban daban a fadin duniya, a sa'i daya kuma, sabon zagayen juyin juya halin kimiyya da fasaha da ci gaban sana'o'i ya haifar da sabon tsarin raya sana'o'in, duk wadannan sun taimaka wajen samar da sabbin dabarun raya tattalin arzikin duniya, tare da habakar cudanyar tattalin arzikin duniya, ban da haka kuma, ana kara fuskantar matsalar tafiyar da harkokin cinikayyar bangare daya da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, haka kuma ana fuskantar matsalar gudanar da tsarin harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, ci gaban bil Adama shi ma ya gamu da matsalar rashin tabbaci da zaman karko.

Shugaba Xi Jinping ya yi bincike da tunani sosai kan sauyin da tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa ke fama da shi, a matsayinsa na shugaban kasa mafi girma ta biyu ta fuskar tattalin arziki da ma kasa mai tasowa da ta fi girma a duniya. A jawabin da ya gabatar a babbar hedkwatar MDD da ke Geneva a watan Janairun shekarar 2017, Xi ya taba yin tambayar cewa, "Me ke faruwa a duniya? Me ya kamata mu yi?" Bugu da kari, ya taba bayyana ra'ayinsa a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" a watan Mayun shekarar da ta gabata, inda ya ce bambancin ra'ayi kan neman zaman lafiya da bunkasuwa da tafiyar da harkokin kasa da kasa babban kalubale ne da ke gaban bil Adama. A wannan karo ma dai, Xi ya gabatar da dabarun Sin kan yadda za a kau da bambancin ra'ayi a fannoni hudu yayin da yake jawabi a Paris. Duk wadannan lamuran sun shaida cewa, ko da yaushe shugaba Xi ya mai da hankali kan raya makomar bil Adama ta bai daya da ma samun nasara da more sakamako tare. Shi mutum ne mai kaunar al'ummar duniya da sauke nauyin da ke bisa wuyansa.

A cikin wannan shirin na kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya gabatar da cewa, hanya mafi muhimmanci ta kawar da bambancin ra'ayi a fannin tafiyar da harkokin kasa da kasa, shi ne a mai da hankali kan ra'ayin tafiyar da harkokin kasa da kasa ta hanyar yin tattauna tare wajen tafiyar da harkokin tattalin arziki, gina duniya mai kyau tare da kuma more nasarorin da aka samu, kana jama'ar kasashe daban daban su rika tattaunawa kan harkokin kasa da kasa. Kana abun mafi muhimmanci wajen kawar da bambancin ra'ayi a fannin amincewa, shi ne tsayawa kan ra'ayi daya duk da bambancin dake akwai, da cimma ra'ayi daya da kawar da bambancin dake tsakani yadda ya kamata, da inganta nuna amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da kawar da duk wani shakku da bangarori daban daban ke nunawa juna ta hanyar tattaunawa. Abun da ya fi muhimmanci wajen kawar da bambacin ra'ayi a fannin zaman lafiya, shi ne tsayawa kan sabon managarcin ra'ayin tsaro mai salon samar da hadin kai mai dorewa, kana da kawar da ra'ayin cacar baki da yin takara ba tare da hadin kai ba, da kuma daukar doka a hannu. Abu mafi muhimmanci wajen kawar da bambanci a fannin neman ci gaba, shi ne tsayawa kan yin kirkire-kirkire, da hada kai, da nuna adalci da yin hakuri, da kuma ci gaba da jagorancin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda.

Daga cikinsu, wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da bambancin ra'ayi kan amincewa da juna, wanda ke da ma'anar gaske. Hakan na nuna cewa, ko takaddamar ciniki da ke kara ta'azzara a fadin duniya ko kuma rikicin siyasa da ake fuskanta a sassa daban daban duk sun faru ne a sakamakon rashin amincewa da juna. A lokacin da ake fama da ra'ayin nan na cacar baki, wasu su kan manta da cewa makomar Adam makoma daya ce, lamarin da ya ke gurgunta tushen amincewa da hadin gwiwa da juna a tsakanin kasa da kasa. A game da wannan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a birnin Paris cewa, "amincewa da juna abu ne da zai taimaka matuka ga yaukaka dangantakar kasa da kasa", ya kuma gabatar da cewa, ya kamata a ba da muhimmanci ga yadda ake mutunta juna da amincewa da juna, a kuma inganta shawarwari a tsakanin al'ummun da ke da al'adu daban daban.

Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi ya samu amincewa da goyon baya daga shugabannin kasashen nahiyar Turai da suka halarci bikin rufe dandalin tafiyar da harkokin duniya da Sin da Faransa suka jagoranta tare. Jim kadan bayan da shugaba Xi ya kammala jawabinsa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa "kungiyar tarayyar Turai EU da kasar Sin za su hada kai wajen tinkarar wasu manyan kalubalolin da ake fuskanta a duniya". A nasa bangaren, shugaban hukumar zartarwar EU Jean-Claude Juncker ya bayyana cewa, kasashen Turai da kasar Sin dukkansu na da niyyar karfafa huldar hadin gwiwa a tsakaninsu. Yayin da shugabar gwamnatin kasar Jamus, madam Angela Merkel, wadda ta je kasar Faransa musamman domin halartar bikin rufe taron dandalin, ta yi kira da a gudanar da wata ganawa tsakanin shugabannin Turai da na Sin a shekara mai zuwa. A cewarta, akwai moriyar bai daya a fannoni daban daban tsakanin kasashen Jamus da Sin.

Ina iya cewa, a wannan lokaci, yayin da daukacin yan Adam ke fuskantar bukatar zabi a tsakanin hadin gwiwa da jayayya da juna, gami da tsakanin bude kofa ko kuma rufe kofa, kungiyar tarayyar Turai EU ta dauki wata daidaitacciyar hanya mai dacewa. (Sanusi, Jamila, Kande, Bilkisu, Lubabatu, Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China