A ranar Talata wakilin kasar Sin ya bukaci kasa da kasa da su taimaka wajen inganta yanayin tsaro a yankin manyan tafkuna.
Tabbatar da tsaro a yankin manyan tafkuna, wanda ya shafi tsakiyar Afrika, shi ne kashin bayan wanzuwar zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afrika, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, shi ne ya bayyana hakan ga kwamitin sulhun MDDr.
Tun bayan watan Yulin shekarar 2018, aka fara samun kyautatuwar yanayin tsaro a shiyyar. A daidai lokacin ne kuma shiyyar ke fuskantar wasu kalubaloli, in ji mista Wu.(Ahmad Fagam)