in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Faransa sun yi ganawa
2019-03-26 13:34:58 cri

A jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa binin Paris, fadar mulkin kasar Faransa, inda takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron ya shirya masa wani kasaitaccen bikin marhabin a babbar kofar Arc de Triomphe dake tsakiyar birnin. Daga bisani shugaba Xi Jinping ya tafi fadar shugaban kasar Faransa ta Elysee, don zantawa da shugaba Macron na kasar Faransa.

Yayin zantawarsu, shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin karfafa imani tsakanin kasashen 2, musamman ma a fannin siyasa, sa'an nan ya bukaci a kara yin hadin gwiwa, bisa tushen zumuntar da ke tsakanin jama'ar kasashen 2. Bayan ganawarsu, shugabannin 2 sun gana da manema labaru tare, inda Xi Jinping ya ce,

"Mun yarda cewa, duniyarmu na fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba cikin shekaru 100 da suka wuce. A wannan lokaci, ya kamata kasashen Sin da Faransa, a matsayinsu na manyan kasashe, su yi kokarin lalubo hanyar fahimtar juna, da amfanawa juna, inda za su hada kai, da yin hagen nesa, sa'an nan su samar da karin gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya."

Shugaban na kasar Sin ya kara da cewa,a bangaren harkar siyasa, kamata ya yi, kasashen Sin da Faransa su karfafa hadin kansu karkashin tsarin MDD da na kungiyar G20, da musayar ra'ayi kan wasu manyan batutuwan duniya misali matsalar sauyin yanayi. Sa'an nan, a bangaren hadin gwiwar da suke yi a fannin sana'o'i daban daban, ya kamata kasashen 2 su zurfafa hadin kansu a fannonin yin amfani da makamashin nukiliya, da zirga-zirgar jiragen sama, da ta kumbuna, daga bisani su kara kokarin kulla huldar hadin kai ta fuskokin kirkiro sabbin fasahohi, da aikin gona, da hada-hadar kudi, da kula da tsoffi, da dai makamantansu. Za a aiwatar da wani aikin hadin kai a kasuwannin bangare na 3 bisa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", don ya zama wani misali.

Haka zalika, shugaban kasar Sin ya nanata cewa, kasar Sin tana daukar nahiyar Turai da muhimmanci sosai, kuma ta dade tana kokarin raya huldar dake tsakaninta da kasashen Turai. Kasar Sin tana goyon bayan kasar Faransa, ta yadda za ta kara taka muhmmiyar rawa a fannin jagorantar aikin hadin kan kasashen Turai, sa'an nan Sin na fatan ganin ita ma kasar Faransa za ta yi tasiri don sanya kungiyar tarayyar Turai EU ta kara nuna niyyar raya huldar dake tsakanin ta da kasar ta Sin. Inda Xi Jinping ya kara da cewa,

"Kasar Faransa babbar kasa ce mai fada a ji a nahiyar Turai, don haka, kasar ce da nake dauka da muhimmanci sosai a wannan ziyarar da nake yi a nahiyar Turai. Kasar Sin na son kyautata huldarta da nahiyar Turai. Muna fatan ganin kasashen Turai za su kasance tsintsiya madaurinki daya, kuma su samu ci gaba, domin hakan ya dace da ra'ayinmu na gina wata duniya mai kunshe da bangarori daban daban."

A nasa bangare, shugaban Macron na kasar Faransa ya ce, kasarsa na son hada kai tare da kasar Sin don tabbatar da samun daidaito, da kwanciyar hankali, da tsaro, gami da walwala a duniya. Ya ce,

"Kasar Faransa tana son zama aminiyar kasar Sin, wadda za ta iya dogaro a kanta, kuma huldar dake tsakaninsu za ta dore har abada. Kasashen 2 za su jingine bambancin ra'ayin dake tsakaninsu a gefe guda, don tabbatar da cimma matsaya tsakaninsu, sa'an nan za su kara girmama juna. Za su rika musayar ra'ayi a kullum. Ina da imani kan makomar huldar dake tsakanin kasashen Faransa da Sin."

Shugaban ya ce Faransa za ta halarci dandalin tattaunawar shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da zai gudana a birnin Beijing a watan Afrilun dake tafe, kuma tana son ganin kungiyar EU ta hada manufofinta da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China