in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya sanya hannu kan dokar da ta mallakawa Isra'ila tuddan Golan
2019-03-26 11:45:46 cri
A jiya ne shugaba Donald Trump na Amurka, ya sanya hannu kan dokar da ta mallakawa Isra'ila yankin tuddan Golan da ake takaddama a kai, yankin da kasar ta Isra'ila ta kwace daga Syria a shekarar 1967.

Dokar dai ta ce, "ya dace Isra'ila ta mallaki tuddan na Gola" saboda matakan tsaron da Isra'ila ke bukata" . Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu dai, ya yi na'aman da matakin da Trump ya dauka,yana mai cewa, abu ne na tarihi.

Sai dai ministan harkokin wajen kasar Syria, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, matakin na Trump ya keta 'yancin kasar Syria, kuma gwamnatin Syriar ta yi watsi da shawarar ta Amurka, kana tuddan na Golan za su ci gaba da kasancewa wani bangare na Syria.

Shi ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul-Gheit ya yi Allah-wadai da matakin shugaban Amurka na mallakawa Isra'ila tuddan Golan na Syria. Ya ce, matakin na Trump ya saba dokokin kasa da kasa.

A wani labarin kuma, mai magana da yawun MDD ya bayyana cewa, manufar MDD game da yankunan tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye suna nan daram, ba su canja ba, duk da matakin da gwamnatin Trump ta dauka na mallaka Isra'ila yankunan. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China