in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar ba da agajin jin kai ta yi kira a  taimaka wajen yaki da Ebola a DRC
2019-03-26 10:57:27 cri

Mataimakin sakatare janar na MDD kan agajin jin kai, Mark Lowcock, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa su taimaka wajen yaki da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC, inda ta yi sanadin rayuka 621.

Da yake ganawa da manema labarai tare da neman tallafin dala miliyan 326 na yaki da cutar, Mark Lowcock, ya ce yana ganin al'ummomin duniya ba sa mayar da hankali kan cutar kamar yadda ya kamata.

Ya ce, ana neman tallafin ne domin biyan bukatun agaji na gaggawa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Stephane Dujarric, kakakin sakatare janar na MDD, ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan jawabin Mark Lowcock cewa, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta samu rahoton sama da mutane 1,000 da suka kamu da cutar a arewacin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tun bayan ayyana barkewarta a watan Agustan bara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China