Barr wanda ya bayyana hakan cikin wata wasika da ya aika majalisar wakilai da kwamitin shari'a da majalisar dattawan kasar, ya ce, bincike na musamman da lauyan ya gudanar bai gano cewa, kamfel din Trump ko wani na kusa da shi ya hada baki da Rasha a kokarin ganin an canja alkaluman zaben shugaban kasar na shekarar 2016 ba.
A wasikar, Barr ya kuma ruwaito wani rahoto na sirri da Mueller ya mika a ranar Jumma'a cewa, binciken bai kai ga tabbatar cewa, mambobin yakin neman zaben Trump da gwamnatin Rasha sun tsoma baki a harkokin zaben kasar ba.
Wasikar da Barr ya rubuta, ya karrare da abin da ya kira, "shaida ta karshe" kan binciken da Mueller ya kwashe kusan shekaru biyu yana gudanarwa kan zargin da ake yiwa Rasha na tsoma baki a zaben shugabancin Amurka na shekarar 2016. (Ibrahim Yaya)