in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nisa ba zai hana Sin da Monaco su zama ainihin abokan juna ba
2019-03-24 18:27:12 cri

Bisa gayyatar da shugaban karamar daular Monaco yarima Albert na biyu ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a karamar daular Monaco, ziyarar da ta kasance ta farko da shugaban Sin zai yi a Monaco. Ziyarar ta shugaba Xi ta kuma shaida cewa, za a iya tabbatar da zaman daidai wa daida da sada zumunci a tsakanin babbar kasa da karamar kasa, ko da yake akwai nisa a tsakaninsu.

Idan aka kwatanta ta da kasar Sin dake da muraba'in kilomita sama da miliyan 9.6, kasar Monaco dake dab da bahar Rum, da kudancin kasar Faransa, tana da muraba'in kilomita 2.02 ne kawai, tana kuma daya daga cikin kananan dauloli guda hudu a nahiyar Turai, kasancewarta karamar kasa ta biyu mafi kankanta a duniya. A matsayin ta na wata kasa mai tsarin jari-hujja dake samun ci gaba sosai, kasar Monaco na samun ci gaba a fannonin sana'ar shirya gasa, yawon shakatawa da kuma hada hadar kudi, har ma matsakaicin yawan kudin shiga na al'ummar kasar ya kai Euro dubu 170, hakan ya sa ta kasance daya daga cikin kasashen da al'ummar su suka fi samun yawan kudin shiga a duniya.

A shekarar 2018, a yayin da yake yin shawarwari tare da yarima Albert na biyu a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya ce, ko da yake Sin da Monaco na da nisa, kuma akwai bambanci sosai a tsakaninsu, duk da haka suna tsayawa kan nuna girmamawa ga juna, da zaman daidai wa daida, da hadin kai irin na samun nasara tare, don haka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun bunkasuwa yadda ya kamata. Idan aka waiwayi yadda ake mu'amala a tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, ana iya gano cewa, lallai wannan abin koyi ne wajen hadin gwiwar wata kasa mai ci gaba da wata kasa mai tasowa.

Misali, tun a shekarar 2012, Monaco ta yi hada gwiwa da kamfanin fasahar sadarwa na Huawei na kasar Sin, inda kuma a shekarar 2016, sassan biyu suka kaddamar da sadarwar intanet ta zamani mai saurin gaske. A shekarar 2017 kuma, kasashen biyu sun daukaka sadarwar internet ta tafi da gidanka a kasar ta Monaco da saurinta ya kai Gbps 1. Sai kuma watan Satumban bara, kamfanin sadarwar na kasar Monaco ya kuma cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kamfanin Huawei ta fannin fasahar 5G, matakin da kuma yasa kasar Monaco ta zama ta farko a duniya da aka kaddamar da wannan fasahar zamani a duk fadin kasar.

Ban da fannin fasahar sadarwa, kasashen biyu sun kuma cimma hadin gwiwa ta fannin hanyar biyan kudaden cinikayya ta zamani wato ta hanyar yanar gizo. A watan Yunin shekarar 2017, Monaco ta cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kamfanin Alipay na kasar Sin, domin samar da sauki ga mutanen kasar Sin dake sayayya a kasar ta Monaco.

Monaco a matsayinta na kasar data shahara ta fannin yawon shakatawa, shugaba Xi Jinping ya nuna mata yabo sosai kan aikin data yi ta fannin kiyaye muhalli da kuma raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba. Yana kuma fatan karfafa hadin gwiwar kasashen biyu ta fannonin kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi da samar da makamashi mai tsabta da kare namun daji bisa ga shawarar ziri daya da hanya daya.

A yayin da duniya ke kara dunkulewa waje daya, yadda za'a yi domin daidaita dangantaka tare da sauran kasashe shi ne wani muhimmin batu da ya kamata kowace kasa da kowace kabila ta yi la'akari da shi. Kasar Sin ta ce, duk wata kasa ko babba ko karama, ko mai arziki ko marar arziki, ko mai karfi ko marar karfi, tana da matsayi iri daya da sauran kasashe. Musamman a wannan yanayin da muke ciki, akwai matsaloli da dama wadanda ba wata kasar da zata iya daidaitawa ita kadai da kanta, wadanda suka shafi cinikayya da kimiyya da fasaha da harkokin kudi da muhalli da yaki da ta'addanci da sauransu. Ya kamata kasashe daban-daban su zama tsintsiya madaurinki daya wajen warware matsalolin, da kara samun fahimtar juna don tinkarar kalubale bisa tushen mutunta juna da amincewa da juna.

Wani shahararren masani a tsohuwar daular kasar Sin Malam Confucius ya taba nuna cewa, idan kana son kulla zumunta da wani, ya kamata ka yaba masa bisa abubuwan da ya kware, amma bai kamata ba ka ambaci abubuwan da bai kware ba, hakan zai sa zumuncinku ya karu. A halin yanzu, kasar Sin da kasar Monaco suna mutunta juna da yin hadin-gwiwa bisa tushen kawowa juna moriya, abun da yasa suka zama abin misali ga hadin-gwiwa da mu'amalar da ake yi tsakanin kasar dake tasowa mafi girma da kasa mafi ci gaban tattalin arziki a duniya. (Bilkisu Xin, Lubabatu Lei, Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China