Yau Asabar, gwamnatocin kasashen Sin da Italiya, sun daddale yarjejeniyar fahimtar juna dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya".
Shugaba Xi Jinping da firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte, sun halarci bikin daddale yarjejeniyar. Bisa wannan mataki, kasar Italiya ta zama ta farko a cikin kungiyar G7, da ta daddale yarjejeniya hadin gwiwa dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin.
Tun bayan da shugaba Xi ya gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na farko a shekarar 2013, kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 150 ne suka daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin dangane da shawarar. (Tasallah Yuan)