in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Italiya za su kara sabon kuzari kan tsohuwar hanyar siliki
2019-03-23 17:49:05 cri

A jiya Juma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake ziyarar aiki a kasar Italiya ya yi shawarwari da kusoshin kasar Italiya. Sabo da haka, 'yan siyasa da 'yan kasuwa, da masu aikin al'adu da kuma kafofin watsa labaru, na kasar Italiya sun lura tare da yabawa sosai ga shawarar neman bunkasuwa tare bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" da Xi Jinping ya gabatar. Suna sa ran cewa, shawarar za ta amfana wa kokarin hada yankunan Turai da Asiya da kuma kulla alaka tsakaninsu, ta yadda za ta iya kara sabon kuzari kan tsohuwar hanyar siliki.

Bayan aukuwar rikicin hada-hadar kudi a shekarar 2008, tattalin arzikin kasar Italiya ya taba shiga wani hali har sau biyu a tsakanin shekarar 2008 da ta 2009, da kuma shekarar 2012 da ta 2014. Bisa alkaluman da hukumar gwamnatin kasar Italiya ta bayar a farkon shekarar nan, sakamakon raguwar yawan GDP a karshen rabin shekarar bara, tattalin arzikin kasar zai sake shiga wani hali a karo na 3 a bana.

Yanzu, matakan raguwar darajar kudin Euro da samar da karin kasafin kudi da a kan yi amfani da su wajen farfado da tattalin arziki, ba su iya taka rawa kamar yadda ake so ba tukuna, kasar Italiya ta zura ido ga sauran yankunan kasa da kasa. Amma kungiyar tarayyar Turai wato EU ta nemi kasar Italiya da ta aiwatar da manufar tsuke bakin aljihu kan harkokin kudi, lamarin ya sa aka ta da hankali tsakanin gwamnatin Italiya da kwamitin EU kan batun kasafin kudi. Sakamakon haka, neman abokan hadin gwiwa da kuma kara yin hadin gwiwa tsakaninsu a yankunan dake waje da yankin EU, ya zama wajibi ga gwamnatin Italiya. A shekarar 2017, a lokacin da Paolo Gentiloni, firaministan gwamnatin Italiya na wancan lokaci ya zo kasar Sin, ya halarci taron koli na tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", inda ya bayyana cewa, "kasar Italiya za ta iya zama jaruma a gun wannan gagarumin bikin da kasar Sin ta shirya kuma take mai da hankali sosai,……Wannan wata dama ce mai matukar kyau. Na halarci taron domin bayyana yadda muke mai da hankalinmu kan shawarar."

A watan Agustan bara, wato watanni 2 bayan kafa sabuwar gwamnatin kasar Italiya ke da wuya, kasar ta kafa wata tawagar musamman domin kara kulla huldar hadin gwiwa da kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin kasar Italiya ta kafa wata tawaga musamman domin kula da aikin hulda da wata kasa. Sa'an nan jami'i mai jagorantar tawagar shi ne Michele Geraci, mataimakin minista mai kula da raya tattalin arziki, da manufofi masu alaka da ayyuka da zaman al'umma. Jami'in masanin ilimin tattalin arziki ne, wanda ya iya yaren Sinanci sosai, kuma ya dade yana aikin koyarwa a wata fitacciyar jami'ar kasar Sin.

Bisa matsayinsa na jami'in da ya fahimci muhimmancin kasar Sin sosai, Michele Geraci ya taba bayyana cewa, kasar Italiya ba ta fitar da isassun kayayyaki zuwa kasar Sin, idan aka kwatanta da kayayyakin da kasashe makwabta suke fitar zuwa kasar Sin. Jami'in ya ce dole kasar Italiya ta gyara manufarta, don kara hadin kai da kasar Sin a fannin gina kayayyakin more rayuwa, sa'an nan za ta samu damar fitar da karin tufafi, da injuna, da abinci, da sauran kayayyaki iri-iri zuwa kasar ta Sin.

A nasa bangare, firaministan kasar Italiya mai ci Giuseppe Conte ya bayyana wa majalissun kafa dokokin kasarsa cewa, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin tana haifar da moriya a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kuma moriya ce ta halal, don haka wannan shawara ta dace da moriyar kasar Italiya.

Shiga aikin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kuduri ne da gwamnatin Italiya ta tsai da, kana kuma, kuduri ne da biranen kasar da masana'antun kasar suka tsai da. Bisa labarin da jaridar New York Times ta bayar, a tashar jiragen ruwa ta Trieste da ke arewacin Italiya, masu aikin gine-gine sanye da kayan yin alkafura cikin ruwa, sun sa tubalin wata sabuwar tashar ruwa da za a gina, wadda aka kiyasta cewa, za ta zama wani sansanin kasar Sin a tashar jiragen ruwa ta Trieste. Jami'an wurin sun ce, masana'antun kasar Sin za su hada kai da takwarorinsu na Italiya, za su yi hayar 'yan kwadagon wurin wajen sarrafa kayayyaki, daga baya za a yi jigilar wadannan kayayyaki zuwa sauran sassan Turai cikin jirgin kasa, ko kuma zuwa kasar Sin cikin jirgin ruwa.

Yayin da ya gana da manema labaru tare da shugaba Sergio Mattarella, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Italiya su kara hada manyan tsare-tsarensu tare, su habaka hadin gwiwarsu a fannonin ababen more rayuwar jama'a da rarraba kaya a zahiri a tashar jiragen ruwa, da yin sufuri cikin jiragen ruwa, tare da fito da wasu ayyukan hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", a kokarin ganin al'ummar duniya sun kara cin gajiyar bunkasuwa. (Sanusi, Bello, Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China