Jami'an biyu da suka hada da babban mai bayar da rahoto kan batun wariyar launin fata na MDD Tendayi Achiume, da shugaban ayarin kwararru dake aiki kan al'ummar Afrika Micheal Balcerzak ne suka yi kiran a ranar yaki da wariyar launin fata ta duniya, wadda ake yi a duk ranar 21 ga watan Maris din kowacce shekara.
Kwararrun biyu sun kuma soki hare-haren da aka kai wata masallaci a kasar New Zealand, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane 50 da raunana wasu da dama
Sun jaddada cewa, dole ne kasashe su gaggauta daukar mataki don rage tsana da wariya domin kare mutane masu rauni da kuma tabbatar da daidaito tsakanin mabanbanta fata. (Fa'iza Mustapha)