in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar kwamitin sulhun MDD na ziyarar aiki a Mali da Burkina Faso
2019-03-22 11:20:56 cri

Da yammacin ranar Alhamis tawagar mambobin kwamitin sulhun MDD ta tashi daga birnin New York don ziyarar aiki zuwa kasashen Mali da Burkina Faso.

Makasudin ziyarar tawagar shi ne, domin duba irin nasarorin da aka cimma da kuma bada kwarin gwiwa wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a Mali tun a shekarar 2015, kamar yadda rahoton kwamitin MDD (SCR) ya sanar, wanda babbar manufarsa ita ce tabbatar da samun ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sauran dalilai biyu na ziyarar tagawar sun hada da duba matsayin ayyukan da dakarun hadin gwiwa dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel wato G5 Sahel (FC-G5S) ke gudanarwa, watanni 6 tun bayan kaddamar da harin ta'addanci a hedkwatar tawagar jami'an MDD a tsakiyar Mali a watan Yunin shekarar 2018, da kuma mayar da hankali kan tabarbarewar yanayin tsaro da ake fuskanta a kasar Burkina Faso.

Wannan shi ne karo na 4 na ziyarar tawagar MDD a Mali, tun bayan kafa tawagar gamayyar kasashen duniya ta MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Mali wato (MINUSMA), a shekarar 2013. A baya dai, tawagar ta kai ziyara kasar a watan Fabrairun shekarar 2014, da watan Maris na shekarar 2016, da kuma watan Oktoban 2017, a lokacin ne kuma ta kai ziyarar a Burkina Faso da Mauritania.

Ziyarar dai na zuwa ne watanni uku gabanin sabunta shirin wanzar da zaman lafiyar kasar a watan Yuni. Bayan dawowar tawagar zuwa New York, ana sa ran kwamitin sulhun zai gudanar da taron ministoci game da batun Mali, yayin da babban sakataren MDD Antonio Guterres zai gabatar da jawabi, kana firaministan kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga zai halarci taron.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China