in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasuwa Sinawa sun samar da tallafi ga mazauna yankin da annobar Idai ta yi kamari a Zimbabwe
2019-03-22 11:08:33 cri

Kwanan baya mahaukaciyar guguwar iskar nan ta Idai, ta yi barna mai yawa a yankin dake gabashin kasar Zimbabwe, inda iska da ambaliyar ruwa suka rushe gidaje da gonaki da dama. Kawo yanzu adadin al'ummar kasar da suka rasa rayuka ya riga ya kai 139, kana sama da dubu gomai sun rasa muhallansu, lamarin da ya jawo hankalin Sinawa wadanda ke zaune a kasar, inda kuma suka samar da tallafin kayayyaki ga wadanda suke fama da wahalhalun da annobar ta haifar. .

A ranar 15 ga watan Maris da muke ciki, mahaukaciyar guguwar iska ta Idai ta mamayi yankin gabashin kasar ta Zimbabwe, inda ta rushe gidaje da gonaki da dama, ta kuma jawo zabtarewar kasa mai tsanani a yankin.

Duk wadannan sun sa kasar wadda ke fama da matsalar koma bayan tattalin arziki shan wahala matuka, a don haka ofishin jakadancin kasar Sin dake wakilci a kasar Zimbabwe ya yi kirayi ga Sinawa mazauna kasar da su samar da tallafi ga masu bukata a kasar.

Sinawa mazauna kasar su ma sun nuna kwazo da himma kan aikin. Yayin bikin samar da tallafin kayayyakin da aka shirya a ranar 20 ga wata, jakadan kasar Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun ya bayyana cewa, "Darajar kayayyakin tallafin da za mu samarwa masu bukata na Zimbabwe ta kai dalar Amurka dubu 200, yau ma za mu yi jigilar wasu kayayyaki zuwa ga wuraren da annobar ta yi kamari bisa mataki na farko, nan gaba za mu ci gaba da isar da su zuwa ga masu bukata, kana gwamnatin kasar Sin ita ma za ta samar da taimakon kayayyaki, da kudi ga gwamnatin Zimbabwe. Ban da haka, a cikin shekarar bana da muke ciki, gaba daya kasar Sin za ta samar wa al'ummomin kasar Zimbabwe shinkafa da yawan ta zai kai tan 10165, tare kuma da haka rijiyoyin ruwa 500 a fadin kasar. Kasar Sin tana fatan taimakonta zai cika imanin al'ummomin kasar ta Zimbabwe kan makomar kasarsu, tare kuma da dakile matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu."

Yanzu kungiyar kamfanonin kasar Sin dake Zimbabwe, da hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwa Sinawa dake Zimbabwe, da hadaddiyar kungiyar Sinawa dake zaune a Zimbabwe, da asusun kare namun daji da tsirrai na kasashen Sin da Zimbabwe, suna gudanar da aikin samar da tallafin kayayyaki ga al'ummun yankin dake shan wahala sakamakon masifar guguwar iska ta Idai ke kawo musu cikin hadin gwiwa, kayayyakin da ake samarwa sun kunshe abinci iri daban daban, da tantuna, da barguna, da kananan jiragen ruwa masu aiki da lartarki da sauransu.

Kawo yanzu an riga an kai kayayyakin jihar Manicaland ta kasar, inda aka fi fama da annobar mai tsanani. Kan wannan, sakataren zartaswa na ma'aikatar tsaron kasa da harkokin sojojin da suka ritaya ta Zimbabwe wanda ya halarci bikin samar da tallafin kayayyakin Martin Rushwaya ya bayyana cewa, a lokacin da al'ummomin kasarsa ke bukatar taimako cikin gaggawa, kasar Sin ta samar da taimakonta nan da nan ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya sake shaida cewa, kasar Sin aminiyar gaske ta kasar Zimbabwe ne, a cewarsa: "Ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe, da Sinawa mazauna kasar, sun samar da tallafin kayayyakin da suka kunshi abinci da barguna, duk wadannan kayayyakin sun warware matsalolin da masu fama da bala'in suke matukar fama da su. A don haka gwamnatin Zimbabwe musamman ma ma'aikatar tsaron kasa da harkokin sojojin da suka ritaya ta kasar Sin, sun nuna babbar godiya ga kasar Sin. An ce, ya fi sauki a fahimci ma'anar zumunta, yayin da aka gamu da matsala, yanzu aikin da kasar Sin ke yi ya shaida mana cewa, kasar Sin aminiyar gaske ta kasarmu ne, jama'ar kasar Sin aminan kasarmu ne."

Hakika kamfanonin kasar Sin dake Zimbabwe ba su gudanar da harkokinsu na yau da kullum yadda ya kamata ba, saboda tattalin arzikin kasar bai samu ci gaba kamar yadda ake fata ba, amma yayin da ake gamuwa da wahala, 'yan kasuwa Sinawa sun sanya kokari matuka domin tattara kayayyakin da ake bukata cikin gaggawa a cikin kwanaki hudu ko biyar, mataimakin shugaban zartaswa na kungiyar 'yan kasuwa Sinawa dake Zimbabwe Li Manjuan ta bayyana cewa, kokarin da 'yan kasuwa Sinawa suke yi domin samar da taimako ga masu bukata na yankin da annobar ta yi kamari ya burge ta matuka, tana mai cewa, "Ma'aikatan wani kamfanin samar da garin filawa suna aikin shirya garin gero, domin jigilar sa zuwa ga masu bukata a yankin da annobar ta yi kamari ba dare ba rana, kana wani kamfanin samar da abin sha ya riga ya samar da abin sha kallaba 2400. Yanzu haka zai kara samar da wasu 6000, saboda an ce ana bukatar ruwan sha sosai. Duk wadannan sun nuna cewa, Sinawa suna hada kai domin ceton aminan garinsu na biyu a Zimbabwe, wadanda suke shan wahalar annobar guguwar iska ta Idai."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China