in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karanta wannan littafi, idan ana son tabbatar kasar Sin abokiya ce ko abokiyar hamayya
2019-03-21 21:31:35 cri

A gabanin lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kaddamar ziyararsa a kasar Italiya a yau Alhamis, shugaban makarantar midil ta Rome ta kasar Italiya da dalibansa 8 sun samu wata wasika da shugaba Xi Jinping ya rubuta musu, da wata tsarabar musamman, wato kundi na biyu na littafin "Ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa", dauke da sanya hannun shugaba Xi.

A cikin kundin farko da na biyu na littafin "Ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa", an tanadi sabbin tunani da ra'ayoyi da shawarwari na shugaban kolin kasar Sin. Kawo yanzu, an fassara su zuwa harsunan kasashen duniya 24 inda ake sayar da su a kasashe da yankuna 160 ko fiye. Sakamakon haka, littafin da shugaban kasar Sin ya rububa ya zama littafin da ya fi samun karbuwa a duk duniya a cikin shekaru 40 da suka gabata.

A yayin taron kara wa juna sani na masu karanta wannan littafi da suka hada da 'yan siyasa da 'yan kasuwa da masana da kuma wadanda suka wallafa wannan littafi suna ganin cewa, a matsayin littafin da wani kusa wanda yake daya daga cikin kusoshi mafi tasiri a duniya, wannan littafin "Ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa" ya kasance tamkar wata kafa, inda al'ummomin kasashen duniya za su iya fahimtar nasarar da kasar Sin ta samu, da dalilin da ya sa kasar Sin ta samu bunkasa, har ma da makomar kasar Sin. "Al'umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama", da tafiyar da tsarin mulkin duniya yadda ake fata da dai sauran basira da shirye-shirye na kasar Sin. Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyinsa masu tarin yawa game da yadda yake mulkin kasar Sin da kuma tafiyar da batutuwan dake shafar kasashen duniya baki daya. Dukkansu suna da muhimmanci matuka. A ganin masu karanta wannan littafin, littafin ya kasance kamar wani "mabudi na zinare" dake kulla alaka tsakanin al'ummun kasar Sin da sauran kasashen duniya, za kuma su cimma matsaya daya na jin dadin rayuwarsu a duniyarmu. Sakamakon haka, yanzu wannan littafi ya fi samun karbuwa a wajen fararen hula, musamman matasa.

Hakika, bisa la'akari da yanayin da ake ciki na yadda al'amura ke sauyawa sauri, kasar Sin ba za ta daina hadin gwiwa da sauran kasashe ba, sa'an nan sauran kasashe su ma ba za su iya daina hadin kai da Sin ba. Sai dai kasashe daban daban suna la'akari da wasu tambayoyi, irinsu "kasar Sin abokiya ce ko kuma abokiyar hamayya?" "Mene ne abun da ci gaban kasar Sin zai haifar wa duniya? Alfanu ce ko kuma matsala?" Dangane da wadannan tambayoyi, littafin mai taken "ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa" ya samar da gaskiyar amsoshin da suka dace kan wadannan tambayoyi".

Henry Alfred Kissinger, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, ya taba furta cewa, wannan littafi ya ba mutane damar fahimtar wani shugaba, da wata babbar kasa, gami da tarihin kasar na shekaru kusan dubu 5. A nasa bangaren, tsohon shugaban gwamnatin kasar Jamus, marigayi Helmut Schmidt, ya ce wannan littafin ya ba jama'ar kasashen waje damar nazarin kasar Sin da tarihinta daga fannoni daban daban, ta yadda za a kara fahimtar kasar, da bangarorinta daban daban.

A lokacin da ake fuskantar sauyawar yanayi a duniya, ko da yake ana samun takara mai tsanani tsakanin wasu tunani, da kungiyoyi, lamarin da ya sa ake fuskantar karin hadura. Amma dole a yi kokarin fadada fahimta da amincewa da juna, kafin a iya yanke madaidaiciyar shawara, da zabar hanyar da ta fi dacewa. Sa'an nan wannan littafi ya samar da wata dama mai kyau domin kasar Sin da sauran kasashe daban daban su kara fahimtar juna, da karfafa imani tsakaninsu. Cikin littafin, ba a kaucewa ambaton sabani da matsaloli ba. Maimakon haka, an nuna gaskiya wajen bayyana abubuwa masu wuya da ake fuskanta a kokarin raya kasar Sin da kuma duniyarmu, haka kuma an bayyana yadda kasar Sin za ta tinkari yadda duniya ke sauyawa, da manufofin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke tsayawa a kai a matsayin wanda ya dace da zamani, da biyan bukatun jama'a, da kokarin gudanar da gyare-gyare da bude kofar kasar, gami da mulki cikin yanayi na kwanciyar hankali.

Alal misali, a cikin takardar shirye-shirye guda 10 da kwamitin zartaswa na EU ya kaddamar a kwanan baya, ya nuna cewa, ya kamata EU ta inganta hada kai da kasar Sin a fannonin sauyin yanayi, samun ci gaba cikin lumana da dai sauransu, da kuma kara azama kan kyautata huldar tattalin arziki a tsakaninta da Sin domin kara samun moriyar juna. Hakan ya nuna cewa, EU tana fatan hada kai da kasar Sin, yayin da a hannu guda kuma take nuna damuwa da shakku kan kasar ta Sin. Hakika dai , EU za ta kau da damuwa da shakkun da take bayan da ta karanta wannan littafin da Xi Jinping ya rubuta.

Dalilin da ya sa littafin "Ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa" ya samu karbuwa sosai a kasuwa shi ne masu karatu daga sassa daban daban na duniya sun gano cewa, yadda kasar Sin take tafiyar da harkokinta da kuma shiga aikin tafiyar da harkokin kasa da kasa, ya dace da yadda 'yan Adam suke neman samu, hakan ya taimaka wa jama'ar Sin da na sauran kasashen duniya su fahimci juna. Shugaba Xi Jinping ya sha bayyana cewa, burin jama'a na jin dadin zaman rayuwa, shi ne manufar da muke kokarin cimmawa. Wannan jimla mai saukin fahimta ya bayyana tunanin Xi Jinping na "Ba da muhimmanci ga jama'a" yadda ya kamata, wadda kuma ta samu amincewar kasa da kasa. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sa wannan littafin Xi Jinping da aka fassara zuwa harshen Italiya ya samu lambar yabon musamman na Cesare Pavese ta fuskar adabi. Kungiyar ba da lambar yabon tana ganin cewa, abubuwan da ke cikin littafin "Ra'ayoyin Xi Jinping na mulkin kasa da tafiyar da harkokin siyasa" sun shafi kasar Sin da ma duniya baki daya. Wannan littafi ya haskaka dukkan kasashen duniya masu mabambantan tsarin zaman al'umma wadanda suke matakan ci gaba daban daban, dangane da raya kansu da kuma ci gaban duniya. (Sanusi, Bello, Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China