in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron koli na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na MDD karo na 2
2019-03-21 14:12:13 cri

A jiya Laraba ne aka bude taron koli na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa na MDD karo na 2 a cibiyar taro dake birnin Buenos Aires na kasar Argentina, inda shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashe da yankuna 193 fiye da 1500 suka halarci taron don bada shawarwari kan yadda za a inganta dangantakar abokantaka a tsakanin kasa da kasa, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa don cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030 na MDD.

A shekarar 1978, an zartas da shirin ayyuka na Buenos Aires a gun taron hadin gwiwar fasahohi a tsakanin kasashe masu tasowa na MDD a kasar Argentina, don sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a dukkan fannoni, wanda ya bude aikin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Shekarar bana shekara ce da ta cika shekaru 40 da tsara wannan shiri, don haka a gun taro na 71 na babban taron MDD a watan Yuli na shekarar 2017, an zartas da kudurin gudanar da taron koli na hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa na MDD karo na 2 a birnin Buenos Aires a watan Maris na bana. A bikin budewar taron, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi jawabi cewa,

"A shekaru 40 da suka gabata, shirin ayyuka na Buenos Aires ya haifar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. A cikin shekarun 40, hadin gwiwar ya sa kaimi ga samun ci gaba a kasashe masu tasowa, kana an canja tsarin hadin gwiwa na duniya, da kuma sa kaimi ga tsara burin samun bunkasuwa mai dorewa, da aiwatar da shi yadda ya kamata. A cikin shekarun 40, kasashe masu tasowa sun yi koyi da juna, da samun ci gaba cikin sauri, a sakamakon hadin gwiwar dake tsakaninsu. A bana, mun sake haduwa da juna a birnin Buenos Aires don waiwayar nasarorin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da tattauna sabon canji da hadin gwiwar ya kawowa duniya, da kawo sabuwar dama ga bunkasuwar kasashe masu tasowa, da kuma sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030."

Guterres ya bayyana cewa, taron a wannan karo zai maida hankali ga yadda za a sa kaimi ga cimma ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030, da kuma burin tinkarar sauyin yanayin duniya da aka tsara bisa yarjejeniyar Paris. Yana fatan bangarori daban daban masu halartar taron za su cimma matsaya daya kan kawar da rashin adalci, da sa kaimi ga kyautata tsarin tattalin arziki, da kiyaye muhalli, don samun bunkasuwa mai dorewa, da sarrafa harkokin birane, da samun daidaito a tsakanin maza da mata, da bin ra'ayin bangarori daban daban, da kyautata tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da sauransu.

Shugaban kasar Argentina mai daukar bakuncin gudanar da taron a wannan karo Mauricio Macri ya bayyana cewa, hadin gwiwa muhimmiyar hanya ce wajen zurfafa dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma tsakaninsu da kasashe masu ci gaba shi ne muhimmin aiki wajen cimma burin samun ci gaba tare da samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030 gaba daya. Ya ce,

"Ina fatan za a cimma ra'ayin bai daya kan tinkarar kalubalolin da muke fuskanta, da cimma burinmu gaba daya a gun taron na wannan karo, hakan zai sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma samar da gudummawa ga samun wadata a dukkan duniya."

Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, wadda ta nuna goyon baya da shiga da kuma samar da gudummawa ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua ya yi jawabi a gun taron cewa,

"Sin ta samu ci gaba, domin kasa da kasa sun nuna goyon bayansu, da yin hadin gwiwa tare da ita. Muna son yin kokari wajen daukar alhakinmu bisa matakin samun bunkasuwa, da karfinmu don raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. Za mu kara taimakawa kasashe masu tasowa wajen shiga kasuwar kasar Sin. Sin za ta kara bude kofa a kasashen waje don samar da dama ga kasashe masu tasowa. Haka zalika kuma, Sin tana son daddale yarjejeniyoyin ciniki tare da kasashe masu tasowa, don sa kaimi ga yin ciniki cikin 'yanci da sauki."(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China