in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministar Birtaniya ta nuna bakin ciki kan jinkirta ficewar kasar daga EU
2019-03-21 10:02:59 cri

Firaiministar Birtaniya Theresa May ta fada a jiya Laraba cewa, bukatar da ta gabatar ta neman a jinkirta ficewar kasar daga tarayyar Turai bakin ciki ne ga bangarenta, ta kara da cewa, wannan wani lokaci ne mafi muhimmanci da ya dace 'yan majalisar dokokin kasar sun yanke shawara kan yarjejeniyar da ta gabatar ta ficewar kasar daga tarayyar Turai.

Firaiminitar, a wani jawabin da ta yi kai tsaye ta gidan talabijin din kasar daga fadar Downing Street, bayan da aka samu jinkiri game da bukatar ficewar kasar ta Birtaniya daga tarayyar Turai, ta fadawa al'ummar kasar Birtaniya a duk fadin kasar cewa, "Ina bangaren ku."

"Lokaci ne mafi muhimmanci da ya dace mu yanke shawara," in ji May, ta bukaci 'yan majalisar dokokin kasar da su goyi bayan bukatar yarjejeniyar ta Brexit, wadda a sau biyu 'yan majalisar na yi fatali da bukatar tun a watan Janairu.

Tun da farko a ranar Laraba, May ta rubutawa shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk cewa, tana neman a jinkirta batun shirye shiryen ficewar Birtaniyan daga tarayyar Turai zuwa ranar 30 ga watan Yuni, tana bukatar karin lokaci kafin kammala dukkan shirye shiryen da suka dace domin majalisar dokokin kasar ta kammala jefa kuri'ar amincewa da ficewar kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China