in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa da Sin na da muhimmanci ga Italiya in ji firaminista Giuseppe Conte
2019-03-21 09:53:59 cri
Firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte, ya ce hadin gwiwa tsakanin kasar sa da Sin, karkashin manufar shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya" ya yi daidai da bukatun Italiya.

Mr. Conte ya ce tattalin arziki, da hada hadar cinikayya karkashin wannan shawara da Sin ta gabatar, na bisa ka'ida ta doka, za kuma ta bunkasa ci gaban da kasar ta Italiya ke fatan samu.

Mr. Conte ya bayyana hakan ne ga 'yan majalissar dokokin kasar sa, gabanin taron kungiyar Turai ta EU dake tafe tsakanin ranekun 21 zuwa 22 ga watan nan na Maris, kuma daya daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna yayin taron shi ne hadin gwiwa da kasar Sin.

A wani ci gaban kuma, firaminista Conte, ya tabbatar da aniyar sa ta halartar taro na biyu, na kasa da kasa game da hadin gwiwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda aka shirya gudanarwa cikin watan Afirilu mai zuwa a nan birnin Beijing.

Ya ce halartar taron zai ba shi damar gabatar da mahangar Italiya, da ma sauran kasashen Turai don gane da shawarar "ziri daya da hanya daya", da tasirin hadin gwiwar sassan wajen cimma nasarar ta.

A yau Alhamis ne dai ake sa ran shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai isa kasar Italiya, a ziyarar aiki ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar cikin shekaru 10.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Sin, yayin zayarar ta sa, kasashen biyu, za su nazarci hanyoyin karfafa hadin gwiwar su a sassa daban daban karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya". Ziyarar dai na zuwa ne a daidai gabar da ake hasashen rattaba hannu kan muhimman yarjeniyoyin fahimtar juna game da shawarar ta "ziri daya da hanya daya." Yarjeniyoyin da a cewar Mr. Conte, ba za su kasance wani kalubale ga Italiya don gane da alakar ta da sauran kasashen yammacin duniya ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China