in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmin aikin da kasar Sin ta sanya gaba a wannan shekara
2019-03-20 16:48:54 cri

Taruka biyu da suka kammala a makon da ya wuce, wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, sun samar da tsarin cimma burin da kasar Sin ta sanya gaba, kuma saukaka fatara shi ne babban aikin da dukkanin al'ummar kasar za su hada kansu wajen gudanarwa.

A yayin da yake halartar tarukan biyu na wannan shekara, sau da dama ne shugaba kasar Sin Xi Jinping ya ambaci batun saukaka fatara, inda kuma ya jaddada cewa, shekaru biyu ne kawai suka rage wajen cimma burin da kasar ta Sin ta sanya gaba na saukaka fatara ya zuwa shekarar 2020, kuma ya zama dole a tsaya ga aiki ba tare da kasala ba. Burin da kasar Sin ta sanya gaba shi ne gina al'umma mai wadata daga dukkan fannoni ya zuwa shekarar 2020, don haka, aikin da za a yi a bana yana da muhimmancin gaske ga cimma burin, wanda ya zama dole a cimma nasararsa.

Kawar da talauci kalubale ne mafi tsanani da ake fuskanta a duniya, kasar Sin ta riga ta cimma babbar nasara a fannin. Bisa kididdigar da bankin duniya ya yi aka nuna cewa, ko wadanne 100 da suka kawar da talauci a duk fadin duniya, 70 daga cikinsu sun fito ne daga kasar Sin. Daga shekarar 1978 zuwa 2017, Sinawa sama da miliyan 700 suka kawar da talauci bisa ma'aunin talauci na duniya ta hanyar gudanar da manufar bude kofa ga kasashen ketare da yin kwaskwarima a cikin gida, da bunkasa tattalin arziki.

Yawan gudummowar da Sin ke samar kan sha'anin kawar da talauci na duniya ya wuce kashi 70 cikin dari a cikin shekaru 40 da suka gabata, haka nan kasar Sin ta kasance kasar da ta fi samun mutane masu kawar da talauci a duniya. Babban daraktan kungiyar abinci da aikin gona ta MDD, wato FAO José Graziano da Silva ya taba bayyana cewa, wa'adin kudurin Sin na kawar da talauci na tafe nan da shekaru 10 gabanin burin MDD na cimma muradun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. Tsohon shugaban bankin duniya Kim Yong yana ganin cewa, aikin kawar da talauci na kasar Sin yana daya daga cikin manyan ayyuka a tarihin dan Adan.

Amma a sakamakon bambancin tarihi, da yanayin halittu, da yawan mutane, da rashin daidaito a fannin tattalin arziki a tsakanin yankuna, mutane fiye da miliyan 10 suna fuskantar talauci a kasar Sin. Bisa kididdigar da hukumar yin kididdiga ta kasar Sin ta yi, ya zuwa karshen bara, yawan mutane masu fama da talauci a kauyukan kasar Sin ya kai miliyan 16 da dubu 600. Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin kara rage yawan masu fama da talauci fiye da miliyan 10 a bana. Cimma wannan buri yana da nasaba da cimma burin kawar da talauci, da samun wadata a dukkan zamantakewar al'ummar kasar Sin a shekarar 2020. Sin ba ta taba cimma irin wannan buri a lokacin da ba.

Don hakan, shugaba Xi Jinping ya bayyanawa wakilan jama'ar kasar Sin a yayin manyan taruka biyu na bana cewa, ya kamata a kara yin kokarin kawar da talauci a mataki kusan karshe. Wannan ya shaida kara yin kokari wajen kawar da talauci, kana ya shaida imanin Sin na cimma burin kawar da talauci cikin lokaci. Kawo yanzu kasar Sin ta shiga mataki na karshe yayin da take kokarin cimma burin kawar da talauci daga duk fannoni a fadin kasar. A don haka ta ci gaba da daukar matakan yaki da talauci tare kuma da aiwatar da manufar farfado da kauyuka, a takaice dai, ana iya cewa, matakan da take dauka sun hada fannoni shida: sauke nauyin tabbatar da tsaron abinci a kauyuka, da ingiza gyaren fuska kan tsarin samar da kayayyakin aikin gona, da kara yayata manufar raya tattalin arzikin kasar ba tare da gurbata muhalli ba, da kara gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kauyuka, da kara kyautata aikin gudanar da harkokin kauyuka, da kuma cimma burin farfado da kauyuka ta hanyar kara zurfafa gyaren fuska.

Duk wadannan matakai ne da gwamnatin kasar Sin za ta dauka yayin da take kokarin yaki da talauci a cikin shekaru biyu masu zuwa. Kana gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin yaki da talauci ta hanyar samar wa masu fama da talauci damammakin shiga kamfanoni neman samun aikin yi a ciki, duk wadannan hakikanan matakai ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka, domin cimma burin kawar da talauci daga duk fannoni nan da shekarar 2020 wato shekara mai zuwa.

Bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, nasarar da kasar Sin ta samu a fannin kau da talauci, da ayyukan da take gudanar da su a kokarin cimma burinta na kau da talauci baki daya a kasar zuwa shekarar 2020, dukkansu sun kasance babbar gudunmowa ga aikin rage talauci a duniya. Hakan ya nuna yadda kasar take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, da yadda take aiwatar da matakai bisa shawarar da ta yi ta kafa "al'ummar bil Adama mai kyakkyawar makoma ta bai daya".

Wajen taron shugabannin duniya na rage talauci da neman ci gaba na shekarar 2015, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi wani jawabi, inda ya ba da shawarar gaggauta gudanar da aikin rage talauci a duniya. Ya ce shekaru 15 da za su bi bayan shekarar 2015, suna da muhimmanci matuka ga kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa, domin a wadannan shekaru ne za su samu damammaki na raya kansu. Saboda haka, kasar Sin za ta yi kokari tare da sauran sassan duniya don kyautata huldar hadin kai, gami da neman ci gaba da ta kasance tsakanin kasashe daban daban. Sa'an nan za ta sa kaimi ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, da ma hadin kan da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, don samar da isassun damammakin da ake bukata wajen gudanar da aikin rage talauci.

Sakwannin da aka samu wajen tarukan majalissun kasar Sin na bana sun sheda wa duniya cikakkiyar niyyar kasar ta Sin a fannin kau da talauci, da yunkurinta na sauke nayin dake bisa wuyanta, da yadda take kokarin daukar takamaiman matakai. A wannan lokaci mai muhimmanci, kokarin gudanar da aiki na rage talauci, shi ne alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wa jama'ar kasar, sa'an nan zai kasance sabuwar gudunmowa da kasar za ta yi wa duniya. (Lubabatu, Bilkisu, Zainab, Jamila, Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China